Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

An Yi Taron Kasa Na Jam'iyyar ANDP Ta Nijar


Mahamadou Issoufou, Shugaban Kasar Nijar
Mahamadou Issoufou, Shugaban Kasar Nijar

A Jamhuriyar Nijar jam’iyyar A.N.D.P Zaman Lafiya ta yi babban taron ta na kasa a Maradi bisa taken Sasantawa, Hadin Kai da kuma Zaman Lafiya.

A safiyar yau asabar shugaban jam’iyyar Musa Adamu Jarmakwai ya bude babban taron na kasa a Maradi.

Wakilin Sashen Hausa na Muryar Amurka a Maradi Chaibou Mani ya tattauna da Mahaman Lawali Gwandah Dan Majalisar dokokin kasar Nijar mai wakiltar jahar Maradi a karkashin jam’iyyar A.N.D.P Zaman Lafiya.

Sun tattauna batutuwa da dama da suka hada da yadda jam’iyyar ke gudanar da ayyukanta, da kuma kawancensu da jam’iyya mai mulkin Kasar Nijar. Mahaman Lawali Gwandah ya fara ne da bayyana matukar jin dadinsa da yadda babban taron ya gudana.

please wait

No media source currently available

0:00 0:02:19 0:00

Tambayoyin wasu ‘yan kasashen Afirka akan manufifi da Shugabancin Donald Trump ga kasashensu
please wait

No media source currently available

0:00 0:09:10 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
XS
SM
MD
LG