Gwamnatin Jamhuriyar Nijar ta tabbatar da cewa an kashe sojojinta guda 46 da kuma fararen hula 28 a karshen makon da ya gabata bayan da dakarun kasar suka fafata da mayakan Boko Haram a kokarin kubutar da wani tsibiri da ke yankin tafkin Chadi.
Jami’an tsaro sun ce sun kashe mayakan ta’addar guda 156 a arangamar da suka yi, wacce ta faru bayan da kungiyar Boko Haram ta kai wani farmaki a tsibirin Karamga a ranar asabar da ta gabata wanda dakarun kasar Nijar din suka ce tuni sun kwato ikon tsibirin.
Kwanan nan kasashen Nijar da Najeriya da Chadi da kuma Kamaru, suka kaddamar da wani samame akan ‘yan kungiyar. ‘Yan kungiyar Boko Haram sun yi sanadiyyar mutuwar mutane sama da dubu goma da kuma raba fiye da mutane miliyan daya a Arewacin Najeriya da muhallansu.