'Yan adawa na jam'iyyar ARDR bagaren Kabir Madarunfa sun balle daga jam'iyyar sun canza sheka zuwa jam'iyyar PNDS dake mulkin kasar.
Malam Hadi Na Abu kakakin mutanen da suka canza sheka yace adawa ba abun alheri ba ce. Yace ya kamata su dawo cikin gwamnati saboda kokarin da ake yi masu. Wai sun gani a kasa dalili ke nan da suka yanke shawarar bada goyon bayansu ga gwamnatin Issoufou. Yace duk shugabannin jam'iyyarsu na yankunan kasar sun canza sheka domin su taimaka Shugaba Issoufou ya samu ya zarce a zaben shekara 2016.
Malam Iro Sani dan asalin yankin Madarunfa din kuma daya daga cikin shugabannin PNDS ya yaba da karbuwar da aka yiwa sabbin shigowa jam'iyyarsu. Yana acewa ita siyasa amana ce kuma wadanda suka kawo masu amana sun karbeta hannu biyu kuma zasu kareta. Yana fatan Ubangiji ya barsu tare su kara samun karfin tafiya ta cigaba da yin ayyukan da zasu taimaki jiharsu ta Madarunfa.
To saidai Malam Yahaya Ari mai adawa na bangaren Sidi Umaru cewa yayi duk wani kauce-kauce ba zai tada masu hankali ba. Ko menene zasu yi su yi zasu cisu a zabe mai zuwa.Duk wadanda suka fitar daga jam'iyyarsu wajen su 49 sun hanasu yi magana da yawun jam'iyya.
Ga rahoton Chaibu Mani.