Rahotanni da dumi-duminsu sun shaida cewa wasu da ake kyautata zaton 'yan kungiyar Boko Haram ne sun kai hari a N'Djamena, babban birnin kasar Chad.
Muryar Amurka ta zanta da Malam Sanusi mazaunin birnin kuma ganau.
Malam Sanusi ya tabbatar cewa an kai hari har a wurare biyu. Harin farko an kai ne akan babban ofishin 'yan sanda dake birnin N'Djamena. Hari na biyu kuma an aunashi ne akan babbar makarantar da ake karantar da aikin 'yansanda.
Harin farko wadansu mutane ne akan babur suka taho da mugun gudu suna son su shiga harabar ofishin 'yansandan. Da aka tsaresu sai daya daga cikin mutanen ya tayar da bom dake tare dashi. Nan take 'yasanda da fararen hula da yawa suka rasa rayukansu.
A makarantar koyas da 'yansanda kuma wani mutum ne ya je ya ajiye wata mota. Bayan ya tafi sai bom ya tashi a motar. Dalibai da suke koyon aikin 'yansanda da dama suka mutu tare da fararen hula masu wucewa.
Bisa ga rahotanni mutane 27 suka mutu kana 101 suka jikata. Gwamnatin kasar ta nemi taimakon jini daga jama'a.
Ga karin bayani.