Wani babban kalubale da ke fuskantar wannan matsala shi ne babu isashun magani da za a baiwa masu fama da wannan cuta da ke addabar birnin na Yamai da kewaye.
“Na farko dai, tun watan Janairu aka samu rahoton cewa an samu bullar wani sabon irin ciwo na sankarau wanda ya shigo a jamhuriyyar Niger, ana tsammanin za a dauki matakai, sai gashi ana neman maganin da za ayiwa mutane shaushawa a duniya babu.” In ji Mustapha Kadi, shugaban kungiyar farar hula a birnin Yamai.
Shi kuwa Malam Adamu wani jami’in kiwon lafiya ne a birnin na Yamai, ya kuma ce cutar ta zo da wani irin yanayi a kasar.
“Cutar ta zo a cikin wani lokaci da babu magani kamar yadda gwamnati ke fadi, an samu maganin amma kadan ne.” In ji Malam Adamu.
An ya yi kokarin jin ta bakin ministan kiwon lafiya na Niger, Manu Agali domin a ji tsokacin da zai yi, sai dai ya zuwa lokacin hada wannan rahoto bai amsa kiran da aka yi mai ta wayar salula ba.