Iyalan dai sun daukaka karar kisan tsohon shugaban ban ne domin a tilastawa gwamnatin Niger yin bincike tare da hukunta wadanda ke da alhakin yin kisan.
“Tun da aka kashe shi babu abin da aka yi, ko barazana ba a yiwa wadanda suka yi kisan ba, ba a musu komai ba.” In ji lauyan iyalan mai suna Abdurrahman.
Da aka tambaye shi ko me urwagidan marigayi Ba’are ta ce a gaban kotun, sai ya ce “ta fada musu abin da yake cikin zuciyarta ne, saboda ya kai shekara 16 suna tambaya amma babu wata kotu da ta saurare ta a Nijar sai yau wannan kotun ta ba ta dama.”
Gwamnatin Nijar dai na ganin sasantawa a ba da diyya shi ne abu mafi a’ala maimakon dawo da gaba baya kamar yadda Malam Ibro Zabai, Darektan Shari’a a ofishin sakataren gwamnatin Niger ya ce.”
“Lokacin da wannan abu ya faru babu wanda bai yi Allah wadai da shi ba, mu dukka bani adama ne muna kuma da iyali, mun kuma san abinda ta rasa.” Zabai ya ce.
Baya ga haka darektan ya ce akwai doka wadda ta ce an shafe wannan zance wadda ta nuna babu bukatar a gurfanar da wani a gaban kotu.
“Idan aka ce mu gurfanar da mutane a gaban kotu kamar mun taka dokar kasar Nijar ne.” Ya kara da cewa
Da aka tambaye shi ko za su biya diyya sai ya ce “in hakan suke so yanzu ma sai mu tafi mu sasanta ai dukkanmu ‘yan Nijar ne. Wannan bawan Allah ya rasa rayuwar shi a cikin aikin tafiyar da ayyukan kasar Niger ne, don haka ba muga matsala ba idan an ce a baiwa iyalin shi diyya in ya kama a basu.”
An dai kashe Ibrahim Ba’are Mai Nasara ne a shekarar 1999 a lokacin da masu kare lafiyarsa suka bude mai wuta a wani filin jirgin saman Yamai.
Yanzu dai kotun ta ECOWAS ta ce za ta yanke hukunci a ranar 19 ga wata mai zuwa.