Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

JAMHURIYAR NIJAR: Malaman Kananan Makarantu Sun Gudanar da Addu'ar Zaman Lafiya


Shugaba Mahamadou Issoufou na Jamhuriyar Nijar
Shugaba Mahamadou Issoufou na Jamhuriyar Nijar

Malaman kananan makarantu a jamhuriyar Nijar sun gudanar da addu'ar neman zaman lafiya da biya masu bukatunsu

Daruruwan malaman kwantiragi na kananan makarantun jamhuriyar Nijar suka fito domin gudanar da sallah da addu'o'i Allah ya kawo kwanciyar hankali a kasar da kuma biya masu bukatunsu.

Kawo yanzu gwamnatin Nijar ta kasa biyan albashinsu kan lokaci. Wasunsu sun yi sallar eidel fitr babu ko kwandala a hannunsu saboda ba'a biyasu ba. Wasu na tsoron za'a iya fiddasu daga gidajen haya.

Mai watsa labaran kungiyar malaman gefen mata Malama Maryama ta kara haske akan dalilin fitowarsu.Tace sun kirasu ne ganin yau 24 ga watan Yuli basu ji komi ba kamar yadda ba'a biyasu albashin watan Yuni ba duk da alkawarin da gwamnati tayi na biyansu kowace ranar takwas ga wata. Gashi yau 24 ga wata ba'a ce masu komi ba. Malaman ma suna jin kunyar bin wasu wurare saboda basukan da ake binsu.

Gwamnan jihar Malam Audu Mamman yace sun dauki matakin warware matsalolin malaman kwantiragi. Duk wanda bai samu albashinshi ba zai samu nan da zuwa Litinin. Ya rokesu su kara hakuri. Idan akwai kudi zasu samu amma idan an samu 'yar matsala kadan su gane su yi hakuri.Babu dadi a ce lokacin albashi ya kai ba'a biya ba.

Ga rahoton Shaaibu Mani.

please wait

No media source currently available

0:00 0:02:33 0:00
Shiga Kai Tsaye

Masana akan manufofin 'yan takarar biyu na shugaban kasar Amurka a takaice
please wait

No media source currently available

0:00 0:03:56 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
TASKAR VOA: Ra’ayoyin Amurkawa Kan Matsayar Trump, Harris Ga Mallakar Bindiga
please wait

No media source currently available

0:00 0:03:40 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
XS
SM
MD
LG