Fashin Baki Kan Dalilan Juyin Mulki A Nijar Da Yunkurin ECOWAS Na Daukar Mataki

  • Murtala Sanyinna

Sojojin CNSP da suka yi juyin mulki a Nijer

A cikin gwamman shekaru da suka gabata, an yi tsallen murna da kasancewar akasarin kasashen yankin Afirka ta yamma da ta tsakiya sun kama turbar tsarin dimokaradiyya, wanda ke samar da shugabannin kasashe na farar hula ta hanyar zabe.

To sai dai murna na neman komawa ciki, a yayin da a ‘yan shekarun baya-bayan nan, sojoji suka soma dawowa suna dauki dai-dai, tare da sake kwace mulki ta hanyar hambarar da zababbiyar gwamnatin Dimokaradiyya.

A cikin shekaru 2 na baya-bayan nan, sojoji sun yi juyin mulki a kasashen Mali, Guinea, Burkina Faso da Chadi, sai kuma a wannan makon ta tashi a Jamhuriyar Nijar, inda shugaban askarawan tsaron fadar shugaban kasa da kan sa, ya juye ya zama madugun hambarar da shugaban da yake karewa.

Janar Abdouramane Tchiani

Mai fashin baki kan lamurran siyasar duniya Farfesa Tukur Muhammad Baba na jami’ar tarayyar Najeriya ta Birnin kebbi, yana ganin wannan babban koma baya ne ga burin da ake da shi na tabbatar da wanzar da tafarkin dimokaradiyya a nahiyar ta Afirka.

Ya ce hakan ya kuma nuna cewa sojoji a kasashen nahiyar Afirka sun riga sun dandani zakin siyasa da mulki, sun kuma manta da babban hakkin da ya rataya a kan su na tabbatar da tsaron kasa.

Bayan ayyana kan sa a zaman sabon shugaban kasar Nijar na mulkin soji, jagoran masu juyin mulki a kasar, Janar Abdurrahman Tchiani, ya lissafo matsalar tsaro da tabarbarewar tattalin arziki da kuma cin hanci da rashawa a zaman dalilansu na kifar da zababbiyar gwamnatin shugaba Muhamed Muzoum, wanda kuma har kawo yanzu suke ci gaba da tsare shi.

To sai dai da alama wadannan dalilan ba su gamsar da akasarin ‘yan kasar ba.

Wasu masu zanga zangar kalobalantar yunkurin kifar da shugaba Bazoum

Wani mai fashin baki kan lamurran yau da kullum a kasar ta Nijar, Abdurrahman Alkasum, yana ganin da akwai abin lura a tattare da wadannan dalilan na juyin mulki da aka bayar.

Alkasum ya ce ai ba yanzu ne matsalolin kasar da aka ambata suka soma ba, kuma shekaru 10 da aka kwashe na gwamnati an yi su ne tare da shi Tciani. shin bai san da matsalolin ba sai yanzu?

Alkasum ya kara jefa ayar tambayar cewa "me ya sa bai hambarar da gwamnatin da ta gabata ba wacce ta kwashe shekaru 8 kan mulki, wadda kuma an ma fi zarginta da ayukan cin hanci da rashawa fiye da wannan?"

Ko baya ga kakkausan suka da Allah wadai da juyin mulkin na Nijar ya fuskanta a duk fadin duniya, wasu rahotanni na cewa akwai yiwuwar kulla wani hadin gwiwa domin tunkarar lamarin.

Shugaban ECOWAS kuma shugaban Najeriya, Bola Ahmed Tinubu

Tuni kuma da kungiyar bunkasa tattalin arzikin kasashen Afirka ta Yamma ta ECOWAS, karkashin jagorancin shugaban Najeriya Bola Ahmed Tinubu, ta sha alwashin daukar tsattsauran mataki, domin maido da Bazoum kan mukaminsa bayan juyin mulkin.

Tsohon Jakadan Najeriayar, Ambasada Jibril Chinade, yana ganin cewa matakin na ECOWAS da kuma musamman Najeriya, yana kan hanya.

Shugabannin kasashen kungiyar ECOWAS/CEDEAO (Hoto: Facebook/CEDEAO/ECOWAS)

To sai dai kuma Janar Abdurrazak Umar, wani mai sharhi kan lamurran tsaro a Najeriya, ya bayyana tababa kan yunkurin na ECOWAS, da sauran kasashen duniya da ke da ra’ayin daukar mataki kan juyin mulkin na Nijar.

To ko ma dai ya ta kare, Farfesa Tukur Baba na ganin cewa wannan juyin mulkin na Nijar da ma na wadansu kasashe da suka gabata, suna tattarre da muhimmin darasi ga shugabannin kasashe na farar hula.

Babbar damuwar da kasashen yammaci musamman abokan hulda da ma manazarta na cikin gida da waje suka bayyana, shi ne yadda juyin mulkin kan iya shafuwar kokarin da ake yi na yaki da ‘yan ta da kayar baya, wadanda rahotanni suka tabbatar cewa sun kutsa tare da yin kaka-gida a kasashen yankin na Sahel.

Saurari sautin rahoton:

Your browser doesn’t support HTML5

Fashin Baki Kan Dalilan Juyin Mulki A Nijar Da Matakin ECOWAS