Buhari ya bayyana haka ne a shafinsa na twitter inda ya bayyana farin ciki da matakin da wanda ya gaje shi Bola Tinubu ya dauka, ya kuma ce yana da kwarin gwiwar cewa shugaban Najeriya zai iya shawo kan matsalar..
Buhari ya ci gaba da cewa, “kamar yadda ake sa zuciya, Ni ma, kamar sauran miliyoyin ‘yan Najeriya, na yi matukar kaduwa da abubuwan da su ka faru a baya-bayan nan a Jamhuriyar Nijar”
Shugaba Muhammadu Buhari ya kuma bayyana damuwa dangane da makomar tsarin damokaradiyya a yankin baki daya da kuma makomar Shugaba Mohammed Bazoum da iyalinsa.
Yace kamar sauran mutane, shi da maidakinsa, sun damu matuka, sai dai ya bayyana jin dadin ganin yadda kungiyar ECOWAS, karkashin jagorancin Shugaba Bola Tinubu ta dauki matakin samar da masalaha, tare da fatar za’a sauya lamarin a kuma kare lafiyar Shugaba Bazoum da iyalinsa.
Dandalin Mu Tattauna