Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Nijar: Abubuwan Da Janar Tchiani Ya Ce A Jawabinsa Na Farko


Janar Abdourahamane Tchiani
Janar Abdourahamane Tchiani

Sojojin da suka kifar da shugaba Mohamed Bazoum a ranar Larabar da ta gabata a Jamhuriyar Nijar sun zabi kwamandan rundunar tsaron fadar Shugaban kasa General Abdourahamane Tchiani a matsayin shugaban majalissar CNSP domin ya jagoranci al’amuran kasar.

NIAMEY, NIGER - A jawabin da ya yi ta kafar talabijin General Tchiani ya zargi hambarariyar gwamnatin ta Nijar da gazawa akan matsalolin tsaro.

Sojojin sun zargi wasu tsofaffin Ministocin Gwamnatin Bazoum da suka buya a ofisoshin jakadancin kasashen waje da yunkurin kai farmaki don fitar da tsohon Shugaban daga inda ake tsare da shi.

Abin da Shugaban Majalisar ceton kasa General de Brigade Abdourahamne Tchiani ya bayyana kenan a kafar television ta RTN mallakar gwamatin Nijar. A jawabinsa na farko ga jama’ar kasar Brigadier General Tchiani ya bayyana cewa lura da yanayin tabarbarewar tsaron da ake ciki a kasar ne mafarin juyin mulkin da ya jagoranta.

Ya ce lalacewar al’amuran tsaron abu ne na zahiri da jami’an tsaro da al’umma ke dandana kudarsu wanda kuma ya haddasa asarar dimbin rayukan jama’a tare da tilasta wa wasu ficewa daga matsugunansu yayinda wasu kuma suka wulakanta.

Munanan hare haren da aka kai a Bosso Inates Chinagoder Anzourou da bakorat da dai sauransu abu ne da ke tunatar wa akan mawuyacin halin da aka shiga.

Ya kara da cewa “salon yakin da ake amfani da shi don tabbatar da tsaron kasarmu duk da kokarin da ‘yan Nijar da ma abokan hulda na ketare suka yi ko kadan ‘yan kasa ba su gamsu da sakamakon ya samar ba, ba zamu ci gaba da aiki da salon da ake ci gaba da aiwatar da shi a halin yanzu ba don kare kasarmu daga barazanar rugujewa”

Ya ce akwai ayar tambayar game da tasirin sakin tarin shugabanin ‘yan ta’addan da mashara’anta ta kulle a matsayin salon yaki a irin wannan hali da muke ciki ba tare da samun tabbacin komai ba.

“Sannan menene ma’ana da manufar kalaman Shugaban dukkan rundunonin mayakan kasa da a bainar jama’a ke cewa kwarewar askarawan dake sadakar da rayukansu don kare kasa ba ta kai ta ‘yan ta’adda ba? Menene ma’anar salon yaki da ta’addancin da a karkashinta aka dakatar da ayyukan hadin guiwa da dakarun kasashe makwafta irinsu Burkina Faso da Mali?”

A fannin tattalin arziki da rayuwar al’umma General Tchani ya ce ayyukan inganta harkokin kudi da na kiwon lafiyar al’umma da ilimi da batun yaki da cin hanci rubda ciki da dukiyar kasa da rashin hukunci na daga cikin fannonin da hambarariyar gwamnati ta gaza inji shi.

A wata sanarwar ta daban wacce Colonel Major Amadou Abdourhamane ya bayar a dazu da sunan Majalissar CNSP na cewa sun sami labarin wasu kusoshin gwamnatin Mohamed Bazoum da suka samu mafaka a ofisoshin jakadancin wasu kasashen waje na kokarin tsara wani abinda zai ba su damar kai farmaki don kwato Shugaba Bazoum daga inda ake tsare da shi.

Sojojin na CNSP sun yi gargadin masu wannan yunkuri su janye kudirinsu domin abu ne da ka iya jefa rayuwar al’umma cikin hadari. Abinda ke nufin har yanzu ana cikin zaman dardar musamman a n’guwanin dake kewayen fadar ta Shugaban kasa ganin yadda rahotanni ke cewa an bukaci masu aiki a irin wadanan wurare da su zauna a gida har sai kura ta lafa.

Saurari cikakken rahoto daga Souley Moumouni Barma:

Nijar: Abubuwan Da Janar Tchiani Ya Ce A Jawabinsa Na Farko. MP3
please wait

No media source currently available

0:00 0:03:21 0:00

Dandalin Mu Tattauna

XS
SM
MD
LG