NAIMEY, NIGER - ‘Yan adawa a kasar na kallon matakin sojojin a matsayin wani abin ishara ga shugabannin kasashen Afrika.
A titunan Yamai babban birnin kasar al’amura sun fara dawowa kamar yadda aka saba inda jama’a ke ci gaba da harakokinsu na yau da kullum ba tare da wata fargaba ba.
Da yake magana a madadin uwar jam’iyar PNDS Tarayya da hantsi, kakakinta na kasa, Iro Sani, ya bayyana cewa babu wata hujjar hambarar da gwamnatin ta shugaba Mohamed Bazoum a bisa la’akari da manyan ayyukan da ta sa gaba da nufin inganta rayuwar ‘yan kasa.
Jam’iyyun adawa a nasu bangare sun kira taron gaggawa a cibiyar jam’iyyar Moden Lumana domin nazari akan wannan al’amarI.
A wata sanarwar da suka bayar ba da dadewa ba sojojin kwamitin CNSP sun ce sun dakatar da ayyukan jam’iyun siyasa sannan sun bayyana rashin jin dadinsu bayan da wani jirgin Faransa ya sauka da sanyin safiyar Alhamis a filin jirgin saman Diori Hamani.
Sojojin sun yi wa Faransar kashedi kan ta mutunta matakin rufe iyakokin kasar da aka dauka a sakamakon wannan juyin mulki.
Wasu majiyoyi sun ce sojojin na tattaunawa domin tantance wanda zai shugabanci kwamitin na CNSP yayin da tawagar jami’an kungiyar CEDEAO ko ECOWAS ke kokarin ganawa da bangarorin.
A daya bangare daruruwan magoya bayan wasu kungiyoyi masu zaman kansu sun yi gangamin a dandalin Palce de La Concertation don ba da goyon baya ga sojojin da suka yi juyin mulki.
Saurari cikakken rahoto daga Souley Moumouni Barma:
Dandalin Mu Tattauna