Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Mataimakiyar Shugaban Amurka Kamala Harris Ta Yi Allah Wadai Da Juyin Mulki A Nijar 


Mataimakiyar shugaban Amurka Kamala Harris
Mataimakiyar shugaban Amurka Kamala Harris

Mataimakiyar Shugaban kasar Amurka Kamala Harris ta yi Allah wadai da yunkurin juyin mulki a Nijar ta kuma bayyana damuwa matuka kan lamarin a wata ganawa da ta yi da shugaban Najeriya Bola Tinubu ta wayar tarho, a cewar wata sanarwa da fadar White House ta fitar. 

Kamala ta amince da Najeriya a matsayin kasar da ke kan gaba a bangaren dimokradiyya da tattalin arziki a nahiyar Afirka.

Sanarwar ta kuma ce Kamala da Shugaba Tinubu sun jaddada kudirinsu na kare dimokradiyya a yammacin Afirka da yankin Kudu da Sahara.

Shugaban ECOWAS kuma shugaban Najeriya, Bola Ahmed Tinubu
Shugaban ECOWAS kuma shugaban Najeriya, Bola Ahmed Tinubu

Kamala ta yi kakkausar suka ga duk wani yunkuri na kwace mulki a Nijar da karfin tuwo, sannan ta jaddada cewa hadin kan da Amurka ke da shi da gwamnatin Nijar ya ta’allaka ne kan ci gaba da jajircewar Nijar wajen tabbatar da tsarin dimokradiyya.

Kamala ta bayyana goyon bayanta ga matakan da Shugaba Tinubu ya dauka na gyara tattalin arzikin Najeriya, da suka hada da kawo karshen tallafin man fetur da kuma daidaita farashin kudaden waje.

Amurka ta ce ta kashe kusan dala miliyan 500 tun daga shekarar 2012 domin taimaka wa Nijar wajen inganta tsaro.

Mohamed Bazoum
Mohamed Bazoum

Shugaban Nijar Mohamed Bazoum dai ya ci gaba da kasancewa a tsare a fadar shugaban kasa da ke birnin Yamai da yammacin ranar Alhamis, kuma ba a san ko wanene ya karbi ragamar mulkin kasar ba, bayan da a yammacin Laraba sojoji suka ayyana yin juyin mulkin.

Faransa da kungiyar kasashen ECOWAS da kuma Amurka sun yi kira da a gaggauta sakin Bazoum a kuma maido da bin doka da oda a kasar. Shi ma Ministan harkokin wajen Rasha, Sergei Lavrov ya ce ya kamata a maido da bin kundin tsarin mulkin kasar.

Juyin mulkin Nijar dai shi ne karo na bakwai a yammacin Afirka da tsakiyar Afirka tun daga shekara ta 2020, kuma zai iya yin tasiri sosai ga ci gaban dimokradiyya, ya kuma janyo koma baya a yaki da ‘yan ta’adda a yankin, inda Nijar ce muhimmiyar kasa da kasashen yammacin duniya ke hulda da ita.

Dandalin Mu Tattauna

Tambayoyin wasu ‘yan kasashen Afirka akan manufifi da Shugabancin Donald Trump ga kasashensu
please wait

No media source currently available

0:00 0:09:10 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
XS
SM
MD
LG