NIAMEY, NIGER - Daruruwan mazauna birnin Yamai ne suka taru a dandalin Place de la Conceration inda suka gudanar da gangamin goyon bayan sojojin kwamitin CNSP wadanda suka bada sanarwar kifar da gwamnatin Shugaba Mohamed Bazoum. Suna masu nuna farin ciki da wannan juyin mulki kamar yadda daya daga cikinsu Gamatche Mahamadou y shaida wa Muryar Amurka.
Masu zanga-zangar sun fantsama titunan birnin Yamai inda a karshe suka nufi ofishin jam’iyar PNDS Tarayya a daidai lokacin da wasu kusoshin jam’iyar ke gudanar da taro. Isar su ke da wuya suka afka cikin ofishin jam’iyar dake n’guwar Zabarkan inda suka kwashi ganima kafin su ka cinna wuta yayin da wasu daga cikinsu suka farfasa gilasai tare da kona motocin da aka kyasta cewa sun kai 30.
Masu sharhi akan al’amuran yau da kullum na cewa har yanzu da sauran hazo a halin da aka shiga a kasar ta Nijar duk da cewa soja sun tabbatar da kifar da gwamnati.
Kawo zuwa lokacin hada wannan rahoto ba a bayyana sunan wanda zai Shugabancin kwamitin CNSP na sojojin da suka kifar da gwamnati ba haka kuma ba wani bayani dangane da abinda ke tafe da tawwagar kungiyar ECOWAS a nan birnin na Yamai.
Saurari cikakken rahoto daga Souley Moumouni Barma:
Dandalin Mu Tattauna