Farfasa Attahiru Jega Ya Cika Wa'adinsa a Hukumar Zabe

Farfasa Attahiru Jega

Farfasa Attahiru Jega zai koma Jami'ar Bayero dake Kano ya cigaba da aikinsa na malunta

Farfasa Attahiru Jega ya cika wa'adin aiki na shekara biyar a hukumar zabe ko INEC

Farfasa Jega ya jagoranci gudanar da zaben kasa sau biyu wato na shekarar 2011 da na shekarar 2015. Na farko Jonathan ne ya samu nasara na biyun kuma Janar Buhari ne Allah ya ba.

Yau Farfasa Jega ya mika ragamar gudanar da hukumar zaben ga daya daga cikin kwamishanoninsa Ahmed Wali. Shi ma Walin zai yi ritaya watan Agusta.

Ranar 17 ga wannan watan ya rubutawa shugaban kasa cewa wa'adinsa zai kare karshen watan nan. Ya sake rubutawa shugaban kasa cewa zai bar hukumar a hannun Ahmed Wali tun daga yau Yuni 30. Shi ma Walin nan da makonni shida zai bar aiki.

Masana harkokin siyasa na ganin Farfasa Jega ya fi kowane shugaban hukumar sa'a. Duk wadanda suka rike hukumar kafinsa ciresu aka yi. Amma ya zo yayi alkawarin zai yi aiki kuma yayi aikin.

Ga rahoton Nasiru Adamu El-Hikaya da karin bayani.

Your browser doesn’t support HTML5

Farfasa Attahiru Jega Ya Cika Wa'adinsa a Hukumar Zabe - 2' 58"