Zaben dai ya gudana ne a wasu sassan jihar domin raba gardama tsakanin dantakarar PDP Darius Ishaku da ‘yar takarar jam’iyyar APC Hajiya A’isha Jummai Alhassan.
A lokacin da ya ke bayyana sakamakon zaben, shugaban hukumar zabe ta INEC a jihar, Farfesa Mohammed Kyari, ya ce jam’iyyar PDP ta samu kuri’u 369,318 yayin da APC ta samu kuri’u 275,984.
“Saboda haka, bayan da dan takarar PDP Darius Ishaku ya cika dokar samun mafi yawan kuri’u, ya zama shi ne ya lashe zaben.” In ji Farfesa Kyari.
Wakilin Muryar Amurka a birnin Jalingo ya ruwaito cewa Mr. Darius ya gudanar da taron manema labarai bayan da aka bayyana shi a matsayin wanda ya lashe zaben inda ya nuna godiyarsa ga wadanda suka zabe shi.
Sai dai a nata bangaren, ‘yar takarar APC, Hajiya A’isha, ta ce ba ta mince da sakamakon zaben ba domin a cewarta an tafka magudi.
A jiya asabar aka sake gudanar da zaben na jihar taraba a sassan wasu kananan hukumomi goma bayan da aka kasa tantance wanda ya lashe zaben farko da aka yi a ranar 11 ga watan nan na Aprilu.