Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

ZABEN2015: Za'a Yanke Hukuncin Kararrakin Zabe


Tambarin INEC
Tambarin INEC

Hukumar zaben Najeriya ta INEC ta tabbatar da cewa kotunan da ke sauraron kararrakin zabe zasu bi kadun masu koke a kuma yanke hukuncin duk wasu kararrakin da ke gabansu.

Kakakin na INEC Nick Dazang ne ya bayyana haka, inda ya kara da cewa suna son a yanke hukunci kafin mika mulki a ranar 29 ga watan Mayu. Barrister Ibrahim Bello ya nuna cewa an wuce matsayin da za a dinga dadewa da shari’ar zabe.

Ya ce yanzu gaba daya da shigar da kara da kuma sauraron karar har zuwa yanke hukunci ba zai wuce watanni uku ba. APC da PD na shirin kai kararrakin zabe.

PDP zata kai kara a jihohin da basu gamsu da zaben ba kamar su Imo da Kaduna da Kano da Zamfara da kuma Nasarawa. Faroukh Gusau kwamitin gabatarwar PDP a Arewa maso Yamma, ya nuna cewa zasu san matakin dauka gama da abinda suka kira manakisar da aka yi musu.

Suma APC zasu kai kara game da zaben Rivers da Gombe da tace an tafka magudi. Shima kuwa dan takarar APC a Jihar Gombe Inuwa Yahaya ya wannan abu ma ya zame musu wata mahangar ganin yadda shari’un zasu kasance.

Mai kare muradun PDP kuwa y ace gwamnonin PDP bas a shayin a kai su kara ko ina. Junaidu Usman Abubakar ya kara da cewa, kowa na da hakkin kai kara kamar yadda suma suke da ikon kare kansu.

XS
SM
MD
LG