An bude rumfunan zabe a daidai lokacin da aka ce za a bude a Jihar Taraba. In dai ba a manta ba an yi zaben gwamnoni a Najeriya ranar 11 ga watan Afrilu shekarar 2015. To amma a wasu jihohin an sami tangardar da ta sa dole aka soke zaben da niyyar sake wa.
Jihohin sun hada dairin su Taraba da Imo. A yau din ake sake zabukan kamar yadda aka sanar daga ofishin hukumar zabe ta INEC. An rarraba kayan a mazabu dari da sittin da biyar da ke Taraba din tare da ma’aikata. Haka kuma an sami isar jami’an tsaro da ke sintirin kare lafiyar al’umma.
Amma a Mazabar Malam Bello an sami wasu matasa da suka far wa jama’ar da suka halarci wajen don yin zabe. Jama’a sun tarwatse don tsira da lafiyarsu. Wasu shedu a wajen sun fadawa wakilin Muryar Amurka cewa, sanadin rikicin shine an sami ‘yan wasu mazabun ne da suka je wajen don yin zabe.
Da aka nemi a hana su yi ne kuma sai hatsaniyar ta kaure inda jama’a suka shiga yin takansu don kar a musu aika-aika. To amma dai a yanzu haka jama’a na ta kada kuri’arsu a kananan hukumomi goma sha shida.