Jam'iyar APC wadda itace ta lashe akasarin zaben da aka gudanar a fadin Najeriya tayi kira ga hukumar zaben kasar wato INEC da ta gaggauta soke wasu sakamakon zabukan da aka gudanar domin sake sababbi bisa zargin tafka magudi.
A wani taron maema labarai da ta gudanar a birnin lagos, hukumar zabe ta kasa banya kwana guda da zaben gwamnoni hukumar zabe wato INEC ta sanar da sakamakon zabukan da akayi na gwamnoni da na 'yan majalisu.
Jam'iyar APC mai shirin karbar ragamar mulkin kasar dai tayi zargin an tafka magudin zabe a jahohin Akwa Ibom da jahar Rivers dake Kudu maso Kudancin Najeriya. A cewar jam'iyar, hukumar INEC ta gaggauta soke wannan sakamakon zaben domin ya saba ma ka'idodin zaben kasar.
A rahoton, kakain jam'iyar ta APC Alhaji Lai Muhammed yace;
"majiyar ta tabbatar mana da cewa fadar shugaban kasa tayi ruwa da tsaki a harkar zaben jahar Rivers da Akwa Ibom inda babban speto na 'yan sandan Najeriya Alhaji Suleman Abba ya tura kwamishinonin 'yan sanda guda biyu domin su sa ido kan wannan zabe ya sami tangarda. Haka mataimaki speto janar 'yan sandan da aka tura daga baya, shima fadar shugaban kasa ta sa a canza shi cikin sa'oi shidda wanda yasa 'yan banga da sauran magoya bayan PDP suke cin karen su ba babbaka. Lamarin ya haifar da satar akwatin zabe da kuma dukan 'yan jam'iyar APC dan haka muke kira da a soke zabe."
Alhaji Lai Muhammed yace irin wannan lamari ya faru a jahar Akwa Ibom inda akasarin masu zabe basu sami takardun zabe ba. Dan haka 'yan jam'iyar sun koka kwarai a cewar ba'ayi masu adalci ba.
Itama jam'iyar PDP a jahar Ogun tace bata amuince da zaben da aka yiwa gwamnan dan takara a karkashin jam'iyar APC ba kuma tayi zargin APC da tafka magudi da kuma hadin baki da hukumar zabe ta INEC dan haka Mr nasiru Isyaka na jam'iyar PDP wanda ya sha kaye yace zai garzaya kotun zabe domin a bi masa hakkin sa.