Daukan matakin ya zama wajibi biyo bayan soke zaben kananan hukumomin Donga, Wukari, Bali, Karamin Lamido, Zin, Takum da Usa.
Kuri'un da aka soke sun fi wadanda aka kirga yawa saboda haka sai an sake zabe a wadannan kananan hukumomin. To saidai ita hukumar zaben ta INEC bata bayyana ranar da zata gudanar da zabe a kananan hukumomin ba.
Chief David Sabo Kente na jam'iyyar SDP yace ba'a yi zabe a wasu wurare ba. Sojoji ne suka cika akwatunan zabe da kuri'u aka je a bada sakamako. Yace jama'ar Taraba zasu yi murna da matakin da INEC ta dauka.
To amma a bangaren Darius Isiaku dan takarar gwamna a karkashin PDP cewa yayi ba abun dadi ba ne domin sun ci zabe sai kuma aka soke. Yace a Donga ba'a yi masu adalci ba domin a rumfunan zabe biyar aka samu matsala cikin guda dari da 'yan kai. Amma yace ko an sake zaben sau goma su ne zasu ci.
Su ma APC cewa suke ce su ne suka ci zabe da an bayyana sakamako su karbi mulki kawai.
Ga rahoton Ibrahm Abdulaziz.