Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

INEC Ba Zata Amince da Bukatar Wasu Jam'iyyun Jihar Rivers Ba


Shugaban Hukumar zabe mai zaman kanta a Najeriya, (INEC) Attahiru Jega.
Shugaban Hukumar zabe mai zaman kanta a Najeriya, (INEC) Attahiru Jega.

Shugaban hukumar zabe ko INEC yace ba zasu amince da bukatar wasu jam'iyyu goma sha shida ba na cewa a cire kwamishanar hukumar ta jihar.

Farfasa Attahiru Jega shugaban hukumar zabe ko INEC yace duk da zanga-zanga da borin da mutane ke yi da kuma bukatar wasu jam'iyyu cewa a cire kwamishanar zaben jihar Rivers ba zasu yi ba.

Farfasa Jega yace ba zata yiwu a dauki matakin cire Mrs Priscila Kan ba, ba tare da kaddamar da bincike ba domin a tabbatar da laifinta kafin a yanke hukunci. To amma hukumar ta tura wasu kwamishanoninta uku domin sa ido a zaben da za'a yi ranar Asabar.

Farfasa Jega yace a Najeriya yiwa mutane zargi abu ne mai sauki. Yace za'a fito a ce wani yayi kaza yayi kaza ba tare da bada hujjoji ba. Yace shi kansa Allah kadai ya san abubuwan da aka zargeshi da yi. To amma sannu a hankali Allah yana wanke mutum. Yace ba zara mutum yayi zargi za'a dauki mataki ba sai an gudanar da kwakwaran bincike a tabbatar zargin gaskiya ne.

Yace kawo yanzu bisa ga binciken da suka yi akwai kurakurai amma basu isa su kaiga cire kwamishanar ba. Dole sai an yi mata adalci. Sai an kirata ta kare kanta. To saidai hukumar ta dauki matakai na sa ido sosai sosai domin a dakile sake aukuwar kowace matsala.. Hukumar zata cigaba da bincike kuma komi ta gano zata bayyanawa jama'a.

Farfasa ya kara da cewa duk wanda ya fadi zabe sai ya rubuto yana neman a sake kwamishanan zabe. Yanzu sun samu irin wadannan korafe-korafen da dama. Kuma su ba zasu yi aiki haka ba.

Kafin hukumar zabe ta soke zaben jiha dole sai akwai hujjoji masu kwari. Idan an ce an yi magudi sai an kawo hujjoji masu yawa yadda zasu shafi sakamakon zaben. Duk magudin da bai taka kara ya karya ba za'a yi anfani dashi ba a soke zabe.

Ga rahoton Umar Faruk Musa.

please wait

No media source currently available

0:00 0:04:11 0:00
Shiga Kai Tsaye

Masana akan manufofin 'yan takarar biyu na shugaban kasar Amurka a takaice
please wait

No media source currently available

0:00 0:03:56 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
TASKAR VOA: Ra’ayoyin Amurkawa Kan Matsayar Trump, Harris Ga Mallakar Bindiga
please wait

No media source currently available

0:00 0:03:40 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
XS
SM
MD
LG