A yau Alhamis hukumar zaben jihar Taraba ta fara raba kayayyakin aiki a wani matakin farko na shirin sake zaben gwamna a wasu mazabu da ke kananan hukumomi goma a jihar.
Kanana hukumomin sun hada da Wukari da Takun da Donga da Ussa da Bali da Karamin Lamido da Ardo Kola da Zing da kuma wata mazaba da ke Jalingo a fadar jihar.
Za dai a sake zaben ne bayan da aka kasa samun tabbacin wanda ya lashe zaben tsakanin Darius Ishaku na jam’iyyar PDP da ke mulkin jihar da kuma Hajiya Aisha Jummai Alhassan da ke takarar a karakashin jam’iyyar APC wacce wasu ke yiwa lakabi da “Maman Taraba.”
“Zaben nan kan za mu ci, domin ina da wannan tabbaci a zuciya ta saboda irin mutanen da muka zagaya muka gani da kuma mutanen da su ke son mu, idan dai ba za a yi magudi ba.” In ji Ishaku.
Ya kuma kara da cewa babu razana ko kodan a cikin zuciyarsa, “ko kadan ban razana ba domin me? mutane suna so na” ya kara da cewa.
To sai dai itama ‘yar takarar ta APC, ta ce babu batun razana a lamarin, “idan ni Allah ya ke so da mulkin nan, duk murdiyar da za su yi na duniyar nan sai mulkin nan ya dawo hanuna, saboda haka babu wata tantama domin mun zage damtse.” In ji Hajiya Aisha.
A dai ranar asabar mai zuwa ake sa ran za a sake zaben wanda ke cike da takaddama, wanda kuma shi ne karo na farko a Najeriya da aka samu mace da ke cikin jerin manyan ‘yan takarar da za su kara.