Babban Kotun Tarayya Ya Bada Oda Kan Suntai

Gwamnan Jihar Taraba, Danbaba Suntai

Wani baban kotun tarayyar Najeriya ya baiwa ministan sharia'r kasar ya bayyana halin da gwamna Suntai yake ciki
Babban lauyan Najeriya Femi Falana kuma dan rajin kare hakin bil adama ya garzaya kotu inda ya kalubali gwamnatin tarayya ta bayyana halin da gwamna Danbaba Suntai yake.

Matakin da Femi Falanan ya dauka ya biyo bayan wasikar da aka ce gwamna Suntai ya rubutawa majalisar dokokin jihar inda ya sanarda majalisar cewa ya dawo ya cigaba da aikinsa. Amma ita majalisar bata amince da wasikar ba tana ikirarin ba shi ne ya rubuta wasikar ba kuma a nata fahimtar bashi da koshin lafiyar da zai iya kama aiki. Ta dalilin haka ta yanke shawarar barin mukaddashin gwamnan ya cigaba da mulki a jihar.

To sai dai a karar da wai shi gwamnan ne ya shigar tare da 'yan majalisar jihar takwas dake goyon bayansa kotun dake saurarar karar ya umurci ministan shari'ar Najeriya ya bayyana halin da gwamnan yake ciki.

A shari'ance lauya Dalong ya ce tun da kotu ya bada oda kan lafiyar Danbaba Suntai ya zama wajibi a kan ministan shari'a ya fito fili ya bayyana yadda gwamnan ya ke. Yin hakan ya zama dole ministan ya tuntubi likitan Danbab Suntai ya bayar da rahoto a likitance da zai mikawa kotun. Ministan shar'ia bashi da wata mafita ko na yi illa ya bi umurnin kotun.

Game da 'yan majalisa takwas dake tare da gwamnan lauya Dalong ya ce yawansu bai kai su goma sha shida ba da suka tsayar da shawarar barin mukaddashin gwamnan ya cigaba. Ya ce babu abun da zasu iya yi. Ya ce idan suna son su tsige gwamnan suna iya yi ba tare da mutane takwas din ba. A akasarin gaskiya su mutane takwas din ba alheri suke yiwa gwamnan ba. Ya ce kamata ya yi su nemi hanyar yin sulhu domin abun da suke yi suna rura wutar rikici ne kawai wanda hakan ba zai haifi da mai ido ba.

Ga karin bayani.

Your browser doesn’t support HTML5

Babban Kotun Tarayya Ya Bada Oda Kan Suntai - 3:45