Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Dambarwar Siyasar Jihar Taraba


Gwamnan Jihar Taraba, Danbaba Suntai
Gwamnan Jihar Taraba, Danbaba Suntai

Jihar Taraba ta shiga wata dambarwar siyasa da ba'a san yadda zata kare ba.

Yayin da ana cigaba da cece-kuce sabili da yadda gwamna Danbaba Suntai ya ki ya bayyana a bainar jama'a sai gashi wai ya fitar da wata sanarwa mai alamun rudani.

Wani hadimin gwamnan mai kula da yada labarai Mr. Sylvanus Giwa ya karanta wata sanarwa daga wata takarda da aka rubuta da hannu cewa gwamnan ya rushe majalisar zartaswa tare da nada kwamishanan sharia na jihar a matsayin sabon sakataren gwamnati da Malam Aminu Jika a matsayin shugaban ma'aikatan gidan gwamnati.

A wani yunkurin tabbatar da zaman lafiya mukaddashin gwamnan Alhaji Garba Umar ta bakin sakataren watsa labarai Mr. Kefas Sule ya kira jama'ar jihar kada su bari wasu su yi anfani dasu su tada fitina sanadiyar dambarwar siyasar da ta kunno kai yanzu a jihar.

Ana cikin wannnan hali sai kuma wasu na hannun daman gwamnan jihar suka ce an rufe majalisar zartaswar jihar. Shi kuma mukaddashin gwamnan ya ce lokci ya yi da jama'a zasu kai zuciya nesa ganin yadda wasu na son tada fitina ko ta yaya.

Duk da buya-buya da ake yi majalisar dokokin jihar ta ce Alhaji Garba Umar ya cigaba da aikinsa na mukaddashin gwamna har sai sun ji daga Danbaba Suntai kuma ya bayyana kansa. Mr. Haruna Tsokwa kakakin majalisar shi ya bayyana hakan.

Ibrahim Abdulaziz nada karin bayani.

please wait

No media source currently available

0:00 0:01:58 0:00
Shiga Kai Tsaye
Masana akan manufofin 'yan takarar biyu na shugaban kasar Amurka a takaice
please wait

No media source currently available

0:00 0:03:56 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
TASKAR VOA: Ra’ayoyin Amurkawa Kan Matsayar Trump, Harris Ga Mallakar Bindiga
please wait

No media source currently available

0:00 0:03:40 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
XS
SM
MD
LG