Wasu majiyoyi dake kusa da tashar saukar jirgin sama a birnin Jalingo, sun tabbatar da cewa akwai wani jirgi da ya sammaci mutane da sanyin safiyar Juma’a.
Wani manomi wanda bai bayanna sunansa ba, ya gana da wakilin Muryar Amurka Ibrahim Abdulaziz.
“Muna gona, misalign karfe goma saura minti biyar sai muka ga wani farin jirgi ya sauka, can wani lokaci sai ga wasu motoci. Motar gaba Hilux ce mai farin fenti, da CR-V da wasu motoci da jami’an tsaro. Daga nan ne aka kai wata bakar mota bakin jirgi.” In ji wani manomi dake kusa da tashar.
Amma hadiman gwamnan sun ki su ce komai, dangane da batun ina gwamnan yake.
Muryar Amurka ya tuntubi hadimin gwamnan na musamman ta fuskar yada labarai Mr. Syvanus Giwa ta waya, amma babu amsa.
Amma wata majiya a cikin gidan gwamnatin jihar ta tabbatar da sulalewar uwar gidan gwamnan Mrs. Hawwa Suntai zuwa Abuja, yayin da mukadashin gwamnan tuni ya cigaba da aiki.
Shi dai mukadashin gwamnan, ya sake komo da ‘yan majalisar zartaswa, da sakataren gwamnati, da ma shugaban ma’aikatan gidan gwamnati, wanda mukarraban gwamnan suka sauke tun farko.