Da amincewar majalisar dokokin jihar Alhaji Garba Umar ya koma kan mukaminsa jiya nan da nan kuma ya mayarda majalisar zartaswar da hadiman gwamna Suntai suka rushe ranar Laraba. Haka ma mukaddashin gwamnan ya mayarda sakataren gwamnati bakin aikinsa da shugaban ma'aikatan gidan gwamna. Haka kuma duk bankuna an umurcesu kada su biya kudin da ba sa hannun mukaddashin gwamnan. Sakataren watsa labarai na mukaddashin gwamnan a wata sanarwa ya ce kowa ya koma bakin aikinsa. Sanarwar ranar Laraba da hadiman Suntai suka yi babu ita, Mukaddashin gwamna shi ne yake rike da iko a jihar Taraba.
A bayanin da majalisar ta bayar ta ce 'yan majalisar sun dauki matakin mayarda Alhaji Garba Umar kan mukaminsa ganin irin halin da gwamna Suntai ke ciki. Sun kara da cewa daukan matakin ya zama wajibi domin tabbatar da zaman lafiya da cigaban jihar. Yayin da yake yiwa manema labari jawabi kakakin majalisar ya ce bayan sun kaima gwamna Suntai ziyara sun dawo sun yi muhawara kan halin da suka ganshi. Ya ce duk wanda yake tsoron Allah dole ya fadi gaskiya. A halin yanzu Suntai ba zai iya kama aiki ba. Don haka yakamata ya koma jinya kada a sa son zuciya ko wani abu.
Mutanen jihar Musulmai da Krista sun yi murna da matsayin da majalisar ta dauka. Sun gargadi jama'a su guji tashin hankali. Sun kara da kiran kwamishanan 'yan sanda ya hukumta duk wani dake son tada hankalin jama'a.
Ibrahim Abdulaziz nada karin bayani.