Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Ina Gwamna Danbaba Suntai?


Gwamna Danbaba Suntai
Gwamna Danbaba Suntai

Shawarar da majalisar dokokin jihar Taraba ta yanke ta sa yanzu ba'a san inda gwamna Danbaba Suntai yake ba.

Bayan shawarar da majalisar dokokin jihar Taraba ta tsayar babu masaniya kan ko ina gwamna Danbaba Suntai yake.

Rahotanni na cewa an yi gaba da shi ganin irin halin da yake ciki. To amma a hukumance babu wanda ya tabbatar da inda ya ke. Sai dai wasu da suke kusa da filin saukar jirgin sama sun ce sun ga wani jirgi fari ya sauka a filin yau safiyar Jama'a.Jim kadan wasu motoci suka isa filin. Sai dai da aka tuntubi sakataren yada labarai na gwamna Suntai Sylvanus Giwa bai ce uffan ba. Amma wata majiya daga gidan gwamnan ta tabbatar da sulalewar matarsa Mrs. Hauwa Suntai zuwa Abuja.

A wata sabuwa kuma Mukaddashin gwamnan Alhaji Garba Umar ya yi taron siri da majalisar zartaswa da jami'an tsaro inda ya nemi mutane su kai zuciya nesa su kuma tabbatar da doka da oda da zaman lafiya. Ya ce kowa ya cigaba da harkar gabansa ba tsahin hankali babu kuma wata tsangwama.

Sai dai kuma 'yan majalisu takwas da suka ki amincewa da abun da takwarorinsu suka tsayar sun ce suna nan kan bakarsu har sai sun ga abun da ya cire ma buzu nadi. Charles Maijankai yana cikin 'yan majalisu da suka ki amincewa da shawarar 'yan'uwansu na cewa gwamna ya koma jinya mukaddashinsa ya cigaba da mulki. Ya ce 'yan majalisa ba sune likitocin gwamna ba. Don haka basu da hurumin cewa ya koma jinya.

Da yake mayarda martani wani tsohon dan majalisa ya ce su wadannan tsirarun ba kasar suke so ba. Aljihunsu da cimma muradunsu suka damesu. Ya ce kowa ya san gaskiya cewa Danbaba Suntai baya cikin lafiya da zai iya karbar mulki. Ya ce abun da ya faru hukunci ne daga Allah kuma ya kamata 'yan siyasa su yi koyi da wannan.

Ga karin bayani.

please wait

No media source currently available

0:00 0:03:32 0:00
Shiga Kai Tsaye
Tambayoyin wasu ‘yan kasashen Afirka akan manufifi da Shugabancin Donald Trump ga kasashensu
please wait

No media source currently available

0:00 0:09:10 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
XS
SM
MD
LG