Yau tun da sanyin safiya mutane suka yi tururuwa zuwa majalisar jihar domin ganin kwakwaf, su ga ko yaya zata kaya game da dawowar gwamnan. Wadanda suka yi dafifi a harabar majalisar sun ce an hanasu shiga kuma sai mai takardar shaida ake bari ya shiga.Mutanen sun ce sun zo ne domin an fada masu cewa gwamnansu ya dawo. Don haka suna son su yi idanu hudu da shi. Sun ce zasu cigaba da tsayawa bakin shiga majalisar su gani ko menene zai faru.
Tun lokacin da gwamnan ya shiga Jalingo fiye da sa'o'i ashirin da hudu har yanzu bai ce uffan ba duk da ziyarar da ake kai masa. Maimakon shi ya yi jawabi matarsa Hauwa Suntai ce ke magana a madadinsa. Lokacin ma da gwamnan jihar Adamawa Murtala Nyako ya kai ziyara matar ce ta karbeshi. Sai dai sakataren watsa labarai na gwamnan ya ce akwai abubuwan da ya kamata a yi kafin gwamnan ya fara jawabi da mutane. A takaice ya fara yin abubuwan da ya kamata ya yi. Da aka fada masa cewa mutane na shakkau da lafiyar gwamnan sai ya ce babu shakku game da lafiyarsa. Ya kara da cewa kafin gwamnan ya dawo ya gayawa Muryar Amurka cewa idan ya dawo ba zai yi saurin yin jawabi ba. Sai ya huta domin gajiyar tafiya mai nisa da ya yi. Ya ce babu hanzari a lamarin. Sakataren ya bada tabbaci cewa nan da 'yan sa'o'i kadan gwamnan zai yi jawabi.
Ga karin bayani.