To sai dai da dawowar gwamnan gida mukaddashinsa ya yiwa jama'ar jihar godiya da yadda suka bashi hadin kai yayin da ya rike madafin ikon jihar. Ya godewa Allah da ya dawo da "maigidansu' ya kuma godewa 'yan jihar yadda suka tarbi gwamnan kuma komi ya tafi daidai.
A zantarwarta da Muryar Amurka matar gwamnan ta hakikance mijinta ya warke. Ta ce ya gama karbar duk maganin da ya kamata. Yana jiran murjewa ne ba wai bai sami sauki ba . Jin saukin shi yasa suka dawo. Idan an sa ido za'a ga abun da zai faru.Ta ce a yi hakuri. Lokaci na zuwa da zai yi magana kuma za'a ga ikon Allah.
A wata sabuwa kuma wai gwamnan ya tura wata wasika zuwa ga majalisar inda yake fada ya dawo ya kama aikinsa sai dai zai dauki hutu na wasu watanni. A wannan makon ne 'yan majalisar zasu zauna su amince ko su ki amincewa da wasikar.
Kawuna sun rabu a jihar. Wasu na son a fito a fada masu gaskiyar lamarin ba tare da rufa-rufa ba.Kamata yayi gwamnan ya kasance agaban 'yan majalisa domin su tantance ko yana da lafiyar da zai iya cigaba da aikinsa.
Ibrahim Abdulaziz nada rahoto.