An Soma Kalamu Kan Zaben Sabon Shugaban PDP

PDP

Bayan saukar Alhaji Bamanga Tukur daga shugabancin jam'iyyar PDP wanda ya maye gurbinsa tamkar matashi ne idan aka kwatantashi da shugaban da ya yi murabus to ko zai iya kawo sabuwar alqibla?
Jam'iyyar PDP ta tsayar da Alhaji Adamu Mu'azu tsohon gwamnan jihar Bauchi a matsayin sabon shugabanta wanda ya gaji Alhaji Bamanga Tukur.

Alhaji Isa Danbirni jigo a jam'iyyar PDP ya ce addu'a ya kamata a yiwa sabon shugaban jam'iyyar Alhaji Adamu Mu'azu. Ya ce bata yiwuwa mutum daya ya biya bukatun jam'iyya sai an hada hannu a yi tafiya tare. A matsayinsa na dan jam'iyyar da ya sha gwagwarmaya domin ganin jam'iyyar ta kafu yana ganin sai an tallafawa sabon shugabn domin ya dinke barakar da ta faru lokacin Bamanga Tukur. Hanyar cin nasara ita ce shugaban ya zama mai sauraran jama'a da bin shawara. Wadanda suka fice har yanzu suna da kafa daya a jam'iyyar. Shi sabon shugaban abokinsu ne. Ya sansu. Sun sanshi domin haka yana iya binsu ya jawo hankalinsu.

Ba shakka Alhaji Ahmed Mu'azu sabon jini ne kwarai to ko hakan zai sa wadanda suka bar jam'iyyar su koma cikinta musamman 'yan kwankwasiya? Malam Rabi Abdullahi Garindanga wani na hannun daman gwamnan Kano Dr Musa Rabiu Kwankwaso ya ce matakin nada sabon jini abu ne mai kyau kuma suna yiwa PDP murna amma a APC su tafiyarsu ta yi nisa. Wasu abubuwa ma da shugabanninsu suka ce a yi ko an yisu yanzu ba zasu koma ba domin bakin alkalami ya riga ya bushe domin shugabanninsu ba masu fada da komawa ba ne. Masu fada da cikawa ne. Shugabanninsu a APC sun samu abokan aiki da abokan gwagwarmaya.

To sa dai Ahmed Aruwa wanda shi ma yana kusa da tsohon gwamnan Kano Malam Ibrahim Shekarau yana da ra'ayi daban. Ya ce magana ta gaskiya ita ce ko sun so ko sun ki sun hadu da cikas domin Alhaji Adamu Mu'azu mutum ne mai hazaka wanda yana aiki tukuru. Zasu yi iyakacin kokarinsu su ga abun da zasu iya yi. Yana iya zagayawa ya lallashi gwamnonin da suka yi fushi domin mafi yawancinsu abokansa ne. Ban da haka Mu'azu sabon jini ne kuma yana da dan farin jini a arewacin Najeriya saboda haka abu ne mawuyaci a ce ba zai iya samun nasara ba. Idan da dan APC na barci da idanu biyu ko ido daya rufe to yanzu ya kwana da idanu bude ya san inda ya nufa. PDP sun dauko tsarin da zasu yi farat da shirin idan an yi wasa. Amma idan APC ta dinke barakar dake cikinta yanzu ta yi adalci watakila za'a yi buga in buga da PDP.

Ga rahoto.

Your browser doesn’t support HTML5

An Soma Kalamu Kan Zaben Sabon Shugaban PDP-3.25