Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Wane Irin Shugaba ne PDP ke Nema?


Shugaban Najeriya Goodluck Jonathan
Shugaban Najeriya Goodluck Jonathan

Yayin da ake jiran PDP ta gayawa duniya sabon shugaba wani mai magana da yawun jam'iyyar ya bayyana irin mutumin da jam'yyar ke bukata.

Yanzu ana jiran jam'iyyar PDP mai mulkin kasar Najeriya ta bayyana sunan sabon shugaban jam'iyyar.

Wani dan jam'iyyar PDP ya ce sun shiga lokacin da gwagwarmaya ta siyasa ta dauki wani karfi domin haka jam'iyyar na bukatan shugaba wanda zai zama natsatstse. Shugaban ya zama mutumin da komi aka gaya masa zai jimre, wato ya yi hakuri. Ya kamata ya zama wanda yake da hangen nesa amma kada a damu da yawan shekaru.

Jam'iyyar ta samu mutumin da idan ya tashi kowace rana yana cikin hankalinsa. Kada ya zama mashayin giya wanda idan ya tashi da safe baya cikin hankalinsa. PDP na bukatar shugaba da zai zama mutumin jama'a, ya zama mutumin da zai iya daukar nauyin jama'a. Yakamata ya zama shugaba mai adalci da tsare gaskiya da guje ma cutar mutane. Kada ya zama mai yankar kayan jama'a ya je aya boye ya ce shi ya samu abun rayuwa.

Ga rahoto.

please wait

No media source currently available

0:00 0:00:49 0:00
Shiga Kai Tsaye
Tambayoyin wasu ‘yan kasashen Afirka akan manufifi da Shugabancin Donald Trump ga kasashensu
please wait

No media source currently available

0:00 0:09:10 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
XS
SM
MD
LG