Sauran wakilank wamitin rikon sun hada da Onarebul Adamu Aliyu dan asalin jam'iyyar CPC da kuma Barrister Ibrahim Hassan Hadeija dan tsohon jam'iyyar ANPP a matsayin sakatare.
To amma wasu 'yan jam'iyyar CPC a jihar sun buturewa kwamitin da aka nada masu. Su dai 'ya'yan jam'iyyar CPC sun yi watsi da kwamitin rikon inda suka kafa sabon shugabanci a karkashin Dr Abubakar Fulata shugaban tsohuwar jam'iyyar ACN a jihar. Alhaji Sarki Kafinta shi aka baiwa mukamin ma'aji na sabon shugabancin Jigawa.
Bangaren Fulata ya ce mutane uku suka zauna suka raba ma kansu mukami ba da yawun mutane ba. Dalili ke nan suka taru kwansu da kwarkwatansu su kalunali abun da mutanen uku suka yi domin idan basu yi haka ba to jam'iyyar APC ita ma zata koma ta zama marasa yin adalci.
To ko bangaren Fulata suna ganin uwar jam'iyyar zata amince da su sai ya ce zata amince da su domin nasu shugabancin na mutane ne ba na mutum uku ba ne.
To amma Barrister Salihu Useni Garin Gabas kakakin kwamitin riko karkashin jagorancin Abubakar Badaru ya ce da mamaki a ce wani ya fito ya ce ya nada wani shugabanci domin wadanda suke da iko a jam'iyyar suka nada nasu shugabancin. Ya ce yaya cikin mutane 31 a tsayar da magana wani ya tashi daga baya ya yi nashi gaban. Ya ce yana tsammanin wasu ne suka shuka wutar rikici a jam'iyyarsu.
Ga karin bayani.