WASHINGTON, DC —
Idan ana wani tunanin gwamnoni da suka fice daga PDP zasu dawo domin Alhaji Bamanga Tukur ya bar kujerar shugabanci gwamnonin sun ce wannan mafarki ne kawai.
Gwamnonin da suka bar PDP sun fara mayarda martani dangane da murabus din da Alhaji Bamanga Tukur ya yi. Wadanda suka shiga jam'iyyar adawa ta APC sun ce sun yi hannun riga da PDP.
Gwamnan Adamawa Murtala Nyako daya daga cikin gwamnonin da suka bar PDP ya ce saukar Alhaji Bamanga Tukur tamkar kashe maciji ne amma ba'a sare kansa ba. Da yake magana ta bakin kakakinsa Ahmad Sajoh ya ce su kan yanzu suna nan daram a sabuwar jam'iyyarsu ta APC. Saukar Bamanga Tukur bata kawo karshen rashin adalci ba da mulkin kama karya da danniya ba. Ya ce su sun fita daga PDP saboda basu goyi bayan zalunci ba.
Tun farko dai shugabannin PDP suka ce zasu tuntubi wadanda suka fice lamarin da yake son ya raba kawunan 'yan jama'iyyar. Wasu 'yan jam'iyyar na ganin a zawarci gwamnonin da suka fice yayin da wasu kuma suna ganin yin hakan bai dace ba. Wasu sun ce tafiyarsu da dawowarsu bai damesu ba. Ko Murtala Nyako ya dawo ko bai dawo PDP ba babu abun da zai canza a harkar PDP a jihar Adamawa. A jihar Adamawa ma sakataren PDP Barrister A. T. Shehu ya ce dawowarsu bai damesu ba. Duk wanda yake son ya shiga jam'iyya ya bi kaida. Rashin son bin kaida ya sa suna fada da Bamanga Tukur. Idan kuma suna son su dawo dama can babu wanda ya koresu.
Ga karin bayani.