Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Sakataren Kwamitin Amintattu na PDP ya ce Wadanda Suka Fice Daga Jam'iyyar Zasu Dawo


Alhaji Bamanga Tukur tsohon shugaban PDP
Alhaji Bamanga Tukur tsohon shugaban PDP

Sanato Walid Jibiril sakataren kwamitin amintattun PDP ya ce ba yau aka fara fita daga jamiyyar ba amma duk da haka sai kara habaka ta keyi don haka wadanda suka fita zasu dawo.

Idan wasu suna ganin jam'iyyar PDP ta ruguje ke nan Sanato Walid Jibril sakataren kwamitin amintattun jam'iyyar baya ganin hakan. Jam'iyyar zata kara habaka kuma wadanda suka fice ma zasu dawo in ji shi.

Yayin da yake jawabi ya lissafa tsoffin shugabannin jam'iyyar da yau babu su. Wasu sun rigamu gidan gaskiya kamar su Solomon Lar wasu kuma suna nan da rai amma jam'iyyar ta cigaba. Ya ce kowace tafiya daga jam'iyyar sai karuwa jam'iyyar keyi. Ya ce a gareshi abubuwan dake faruwa alamomi ne na samun nasarar PDP. Ya ce akwai alamomi cewa mutanen da suka fice daga jam'iyyar zasu dawo.

Sanato Jibril ya cigaba da cewa PDP gidan mutanen da suka fita ne. Sun tafi inda yanzu ana wasa da hankulansu. Ya yi misali da mutumin da ya gina gidan ubansa amma ya tattara ya koma gidan uban wani inda a ke yi masa wulakanci ai sai ya koma gidansa na ainihi da ya taimaka ya gina. Ya ce da yaddar Ubangiji mutanen da suka fice zasu dawo. Ya ce ba zasu yi masu allawadai ba sai dai su roki Allah su dawo gidan ubansu. Ya ce yau kowa na jin dadi har da shugaban kasa. Bamanga ya yi tunanin cigaban jam'iyyar bai je kotu ba ya bar kujerarsa da kansa domin kawo zaman lafiya.

Da aka tambayeshi ko harsashen da wasu keyi na cewa da zarar Bamanga ya bar kujerarsa kofar tunbuke shugaba Goodluck Jonathan ta budu ke nan kuma wai idan shi Jonathan na son jam'iyyar ta rayu ta kai labari gida to kada ya ce zai sake tsayawa takara. Sanato ya ce wai shi Bamanga Tukur shi kadai ne dan Najeriya wanda yake goyon bayan Jonathan?. Wai shi Bamanga shi kadai zai iya sa Jonathan ya ci zabe ko kada ya ci zabe? Ya ce ya kamata mutane su yi la'akari yadda yanayin abubuwa suke. Idan ana ganin kashin Jonathan ya bushe da tafiyar Bamanga to shirme ne da rashin yadda da ikon Allah. Idan yau shugaban kasar bashi ba za'a iya kawo wani ba?

Ga karin bayani

please wait

No media source currently available

0:00 0:03:53 0:00
Shiga Kai Tsaye
Tambayoyin wasu ‘yan kasashen Afirka akan manufifi da Shugabancin Donald Trump ga kasashensu
please wait

No media source currently available

0:00 0:09:10 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
XS
SM
MD
LG