Alhaji Salisu Mamuda shugaban PDP a jihar Jigawa ya ce ya taba fadawa Alhaji Bamanga Tukur cewa PDP a Najeriya bata da matsala. Yanzu abun da ya fada masa ya tabbata. Ya ce tun da wuri abun da ya kamata Bamanga Tukur ya yi shi ne ya shiga kafofin labarai ya nemi ahuwar 'yan jam'iyyar PDP a duk fadin Najeriya. Dalilin yin hakan kuwa in ji Alhaji Salisu shi ne Bamanga Tukur ya shiga jam'iyyarsu ya kusa ya karya masu tsarin jam'iyya. Ya ce Bamanga ya taimaka wurin kawo baraka a PDP. Ya ce tafiyarsa ba ta murna ba ce domin ya yiwa jam'iyyar raunin da har abada ba za'a taba yin shugaban jam'iyya da ya yiwa jam'iyyarsa rauni kamar Bamanga Tukur ba.
A Kano kuma mataimakin kwamitin rikon jam'iyyar PDP na jihar Alhaji Shehu Wada Sagagi ya ce matakin da Bamanga Tukur ya dauka ya nuna dattakunsa a fili.Ya kuma nuna cewa zaman lafiyar jam'iyyar shi ne mafi a'ala a wurinsa. Ya ce su a Kano ko babu komi ba zasu manta da Bamanga Tukur ba domin ya kwato masu jam'iyyar daga inda aka shaketa. Yanzu tana hannun jama'a. Dangane da ko ya makara da yin murabus sai da jam'iyyar ta rasa 'ya'yanta da dama sai Alhaji Shehu ya ce a rayuwa a kan yi fadi tashi, wato a yi sama a yi kasa. Idan jam'iyya ta cika da yawa dole ta yi nunfashi. Ya ce rigingimun su ne nunfashin jam'iyyar. Abun da ya faru ke nan a PDP. Ragowar jam'iyyu da yake kanana ne ai ba'a rigingimu cikinsu. Ya ce tafiyar siyasa ke nan idan ka ji a na tinga-tinga.
Amma Alhaji Salisu Mamuda ya musanta rade-radin da wasu keyi cewa tsohon shugaban PDP ne ya hana gwamnan Jigawa Sule Lamido rawar gaban hantsi a jam'iyyar musamman batun nan na neman kujerar shugaban kasar Najeriya. Ya ce Bamanga bai isa ya hana Sule Lamido tsayawa takarar shugaban kasa ba. Ya ce Sule Lamido ban da zama gwamnan Jigawa yana cikin kwamitin amintattu na jam'iyyar. Kuma shi Sule Lamido bai taba fitowa ya ce zai yi takara ba. Amma 'yan Najeriya masu hangen nesa suna ganin idan Sule Lamido ya fito zai yi abun da ya yi a Jigawa a duk fadin Najeriya.
Ga karin bayani