Wani bangaren jam'iyyar ya yi watsi da bude sabon ofishin lamarin dake nunawa akwai baraka tsakanin 'ya'yan jam;iyyar a jihar ta Neja. Lamarin yanzu dai ya kaisu da samun shugabanni biyu, wato Alhaji Baba Aminu da Ibrahim Bako Shettima. Shi Alhaji Baba Aminu yana da goyon bayan Sanato Ibrahim Musa da sauran 'yan majalisun dake karkashin jam'iyyar.
Shugaban marasa rinjaye a majalisar dokokin jihar Onarebu Nurudeen Umar shi ne jami'in yada labarai na bangaren Baba Aminu. Ya ce a dokar APC wanda yake da gwamna shi ne shugaban jam'iyyar a kowace jiha. Ya ce abun ya bashi mamaki da ya ga Malam Nasiru El-Rufai wanda yana cikin shugabannin kasa na jam'iyyar a wajen taron bude ofishin daya bangaren. Ya ce abun da yake tsammani daga wurin El-Rufai ba shi ya gani ba.Ya zo wurin taron bangaren Shettima kuma bai ga Sanato Ibrahim Musa ba wanda shi ne shugaban jam'iyyar a jihar.
Nurudeen Umar ya kara da cewa duk wandada suka je wurin bude ofishin bangaren Shettima ba 'yan jam'iyyar ba ne domin har yanzu ba'a yiwa mutane ragista ba. Ya ce shi da sauran wasu mutane su ne anihin 'yan jam'iyya.'Yan bangaren Shettima 'yan jeka na yika ne, kuma su ne basa son zaman lafiya.Su na son su kawo bangaranci. Ya ce basu yadda da shugabanci Bako Shettima ba ko kadan domin lokacin da suka yi zabe shi ne na biyu da ya zabi Baba Aminu a matsayin shugaba.
Amma a bangaren Bako Shettima sun ce sun bude ofishin ne a kan ka'ida da kuma sanin uwar jam'iyyar dake Abuja. Mr. Solomon Nyaze jami'in yada labarai na wannan bangaren ya ce su suka samo ofis suka gayyaci shugaban kasa na jam'iyyarsu ya zo ya kaddamar da ofis din. Shi ya aiko mataimakin sakataren jam'iyya na kasa Malam Nasiru El-Rufai ya wakilceshi a wurin kaddamar da ofishin. Ba shi kadai ma ya zo ba. Wasu manyan jam'iyyar sun rufawa Nasiru El-Rufai baya.
Ga karin bayani.