An Sace Turawa Biyu A Birnin Kebbi

Sojoji masu gadin rumfar zabe lokacin zaben gwamna a kaduna ranar 28 Afrilu, 2011.

Hukumomin 'yan sandan Najeriya sun ce wasu 'yan bindiga sun sace dan Britaniya da dan Italiya daga gidansu a Jihar Kebbi daren alhamisa.

‘Yan sanda a Najeriya sun ce wasu ‘yan bindiga sun sace wani dan Britaniya da wani dan Italiya daga gidan da suke zaune ciki a Jihar Kebbi dake arewa maso yammacin Najeriya.

Jami’ai suka ce an harbi mutum na uku aka ji masa rauni a lokacin da yayi kokarin hana satar wadannan mutanen ranar alhamis da daddare a Birnin Kebbi, babban birnin Jihar.

‘Yan sanda suka ce mutanen biyu da aka sace ma’aikata ne na wani kamfanin gine-gine. Suka ce babu wanda ya aika da takardar neman fansa domin sako mutanen.

An saba da ganin sace-sacen mutane a yankin Niger Delta mai arzikin man fetur a kudancin Najeriya, amma irin wannan al’amari ba sabam-ba ne a yankin arewacin Najeriya.

A makwabciyar Najeriya daga arewa ma, watau Jamhuriyar Nijar, an sha sace ‘yan kasashen waje cikin ‘yan shekarun nan. Jihar ta Kebbi tana iyaka da Jamhuriyar Nijar da kuma Benin.