Wata kungiyar rajin kare hakkin dan adam ta ce yamutsin siyasa a Nijeriya ya hallaka sama da mutane 800 a watan jiya, lokacin da fadace-fadace su ka barke sanadiyyar sake zaben shugaba Goodluck Jonathan.
Kungiyar Human Rights Watch da ke birnin New York ta fadi ranar Litini cewa hukumomin sun kasa tsai da yawan tashe-tashen hankali, sannan ta yi kira ga gwamnatin ta yi bincike ta kuma gurfanar da masu aikatawa.
Kungiyar ta ce ta tara hujjojin da ke nuna yadda ‘yan sanda da sojoji su ka yi ta amfani da karfin da ya wuce kima wajen kokarin shawo kan tashin hankali da fadace-fadacen bangarori.
Kungiyar ta ce tashin hankali mafi muni ya faru ne a Kudancin jihar Kaduna, inda shugabannin Kirista da Musulmi su ka gaya wa kungiyar kare hakkin dan adam cewa yamutsin ya yi sanadin mutuwar mutane 500.
Mr. Jonathan ya kafa kwamitin binciken rikicin, ciki har da tantance ko mutane nawa ne su ka mutu, mene ne ya janyo tashin hankalin kuma yaya za a kau da shi nan gaba.