‘Yan sanda a birnin New York a nan Amurka, sun ce su na sa ran gurfanar da shugaban Asusun Lamunin Kudi na Duniya, IMF, gaban kotu inda zasu tuhume shi da laifin neman yin lalatar karfi da yaji, da kokarin yin fyade da kuma tsare ma’aikaciyar hotel a cikin daki ta hanyar da ta saba doka.
‘Yan sanda suka ce sun kama Dominique Strauss-Kahn dan asalin kasar Faransa da maraicen asabar, a lokacin da suka fito da shi daga cikin jirgin saman da sauran ‘yan mintoci kadan ya tashi zuwa Paris a kasar Faransa.
‘Yan sanda suka ce wata mace ‘yar shekaru 32 da haihuwa mai sharar daki a Sofitel Hotel dake New York, ta ce ta shiga dakin da Strauss-Kahn yake da la’asar domin sharewa da gyaran daki. Matar ta fadawa ‘yan sanda cewa Strauss-Kahn ya fito tsirara daga bayan daki, ya kuma yi kokarin tilasta mata ta yi lalata da shi. Ta samu ta tsere daga dakin ta fadawa sauran ma’aikatan hotel din wadanda suka kira ‘yan sanda.
‘Yan sanda suka ce a lokacin da suka isa hotel din, Strauss-Kahn ya riga ya kama hanyar tafiya filin jirgin sama, inda ya bar wayar salularsa da wasu kayansa a cikin dakin. An ce an yi wa matar jinyar rauni maras tsanani a wani asibiti.
Wani kakakin asusun IMF a nan Washington ya ki yin sharhi kan wannan al’amari.
Strauss-Kahn ya zamo shugaban Asusun Lamunin Kudi na Duniya, IMF a watan Nuwambar 2007. Shi ne tsohon ministan kudi na kasar Faransa, kuma ana daukarsa a zaman babban wanda zai kalubalanci shugaba Nicolas Sarkozy a zaben shugaban kasa na Faransa da za a yi a shekara mai zuwa a matsayin dan takarar jam’iyyar gurguzu ta Socialist. Wasu su na fadin cewa shugaba Sarkozy ya goyi bayan Strauss-Kahn ya zamo babban darektan asusun IMF ne ma a wata dabarar kawar da shi daga cikin harkokin siyasar Faransa.
Strauss-Kahn yana auren wata sananniyar ‘yar jarida mai aikin telebijin a faransa, kuma a can baya ma ya sha fuskantar abubuwan fallasa na yin fasikanci. A shekarar 2008 ya nemi gafara saboda abinda shi da kansa ya kira kuskuren tunani a bayan da yayi lalata da wata ma’aikaciyar asusun na IMF.