Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Italiya Ta Koka Da Yadda Aka yi Yunkurin Ceto Wasu Turawa A Najeriya


Daya daga cikin mutanen da aka kashe kafin sojojin Najeriya da na Britaniya su samu nasarar kwato su, Chris McManus dan kasar Britaniya.
Daya daga cikin mutanen da aka kashe kafin sojojin Najeriya da na Britaniya su samu nasarar kwato su, Chris McManus dan kasar Britaniya.

Shugaban Italiya, Giorgio Napolitano, yace Britaniya ba ta fadawa Italiya ko ta nemi shawararta a game da wannan yunkurin ceto mutanen da ya ci tura ba, matakin da yace bai gane dalilinsa ba

Hukumomin Italiya Sun bayyana fusatar cewa an yi yunkurin ceto wani dan kasar ta Italiya tare da wani dan Britaniya da aka yi garkuwa da su a Najeriya ba tare da an nemi shawararsu ba.

A lokacin da yake magana da ‘yan jarida yau jumma’a, shugaban kasar Italiya, Giorgio Napolitano, yace Britaniya ba ta fadawa Italiya ko ta nemi shawararta a game da wannan yunkurin ceto mutanen da ya ci tura ba, matakin da yace bai gane dalilinsa ba.

Shugaban wani kwamitin majalisar dokokin Italiya mai kula da harkokin tsaron kasa, Massimo d’Alema, yace akwai bukata ga Britaniya ta fayyace dalilin da ya sa ba ta tattauna yunkurin ceto mutanen da Italiya ba kafin kaddamar da shi.

Mutanen da suka sace Franco Lamolinara dan kasar Italiya da Christopher MacManus dan kasar Britaniya sun kashe su jiya alhamis a lokacin da sojojin Najeriya da na Britaniya suka yi yunkurin kwato su a birnin Sokoto.

Firayim ministan Britaniya, David Cameron, ya fada jiya alhamis cewa ya amince da a yi yunkurin ceto mutanen a bayan da suka samu bayani na inda ake tsare da su, kuma rayukansu na cikin hatsari mai yawa.

Da alamun Mr. Cameron ya kira firayim ministan Italiya Mario Monti domin shaida masa wannan lamarin, amma kuma sai bayan da aka kaddamar da yunkurin.

Shugaba Goodluck Jonathan na Najeriya ya dora laifin sace mutanen a kan kungiyar Boko Haram, ya kuma ce an kama dukkan mutanen da suka sace su, amma bai fadi yawansu ba.

Aika Sharhinka

XS
SM
MD
LG