Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Kotun Daukaka Kara Ta Dage Fara Sauraron Karar CPC Kan Zaben Shugaban Kasa


Dan takarar shugabancin Najeriya,Janar Muhammadu Buhari mai ritaya.
Dan takarar shugabancin Najeriya,Janar Muhammadu Buhari mai ritaya.

Kotun daukaka kara ta tarayya ta dage sauraron karar da jam'iyyar CPC mai adawa ta shigar,na neman a soke sakamakon zaben shugaban kasa da aka yi cikin watan Afrilu,har aka ayyana shugabab Goodluck,a amtsayin wanda ya sami nasara.

Kotun daukaka kara ta tarayya ta dage fara sauraron karar da jam'iyyar adawa ta CPC ta shigar da ke bukatar soke sakamakon zaben watan afrilu daya bawa shugaba Jonthan na PDP nasara.

Kotun ta dage fara sauraron kararce zuwa litinin 23 ga watan nan na mayu don bawa masu shigarda kara zarafin mikawa kotu wassu muhimman takardun korafi da za a rabawa wadanda ake karar wato jam'iyyar PDP.

Da yake zantawa da manema labarai a harabar babbar kotun daukaka karar lauyan jam'iyyar CPC James Ocholi SAN, yace zasu shigarda bukatu 50 da suke son kotun ta biya musu ciki har da umurtar hukumar zabe ta kawo wassu muhimman takardu don zama shaidu a shari'ar.

Wadannan muhimman takardu dai sun hada da katunan kuri'un da aka kada da CPC ke cewa an yi dangwale ne kawai musamman a jihohin kudu maso kudu da kudu maso gabas.

Lauyan PDP Joe Kerry Gadzama yace zasu bukaci wadannan takardu don shiryawa tsaf su kare nasarar shugaba Jonathan in aka dawo kotu ranar litinin.
Im ba'a manta ba dan takarar CPC Janar Muhammadu Buhari ya ce ba zai sake zuwa kotu ba bayan share wata 50 daga 2003-2007 yana safa da marwa a kotun don kalubalantar PDP ba tare da samun nasara ba.

Don haka jam'iyyar sa ta CPC ta daura gammo don amshe wannan matakin shari'a da zummar kawarda da PDP da tayi kaka gida kan mulki tun dawowa dimokradiyyar jamhuriya ta 3 a 1999.

Tambayoyin wasu ‘yan kasashen Afirka akan manufifi da Shugabancin Donald Trump ga kasashensu
please wait

No media source currently available

0:00 0:09:10 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
XS
SM
MD
LG