Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Mutane dari takwas ne suka halaka a rikicin zaben Nigeria


Wata mata 'yar Nigeria ce ke kallon gidajen da aka kokkona a lokacin rikicin zaben Nigeria a kauyen Kachia, kudancin jihar Kaduna.
Wata mata 'yar Nigeria ce ke kallon gidajen da aka kokkona a lokacin rikicin zaben Nigeria a kauyen Kachia, kudancin jihar Kaduna.

Kungiyar kare hakkin Bil Adama (Human Rights Watch) da cibiyarta ke birnin New York nan Amurka,litinin din nan ta bada rahoton dake cewa sama da mutane dari takwas ne suka halaka a dalilin rikice-rikicen siyasar da suka biyo bayan babban zaben da aka gudanar a watan Afrilun da ya gabata a Nigeria. Mafi munin rikicin shine wanda ya biyo bayan bayyana sakamakon zaben shugaba Goodluck Jonathan.

Kungiyar ta kare hakkin Bil Adama ta kasa da kasa tayi zargin cewa ya zuwa yanzu dai hukumomin Nigeria sun gaza daukan wasu kwararan matakan da zasu hana sake afkuwar rikice-rikicen siyasar bayan zabe, don haka kungiyar ke yin kira ga Gwamnatin Nigeria da ta gudanar da cikakken binciken masu hannu a rikicin domin gurfanar dasu gaban shari’a. Kungiyar tace, ba inda rikicin yafi muni kamar Kudancin jihar Kaduna inda shugabannin kirista da na Musulmi suka shaidawa kungiyar kare hakkin Bil Adama cewa sama da mutane dari biyar ne suka halaka a yankin, mafi yawan wadanda aka kashe Musulmi ne. Shugaba Goodluck Jonathan ya kafa hukumar bincike domin gano abinda ya haddasa rikicin da adadin yawan wadanda suka rasa rayukansu da dukiyarsu.

XS
SM
MD
LG