hukumomin Najeriya sun kafa kwamitin bincike wadda zata binciko da nzarin abinda ya janyo hargitsin dake da nasaba da siyasa a babban zaben da aka gudanar a Najeriyan a watan da ya gabata.
Shugaba Goodluck Jonathan, Laraba yake bayanin cewa hukumar binciken mai wakilai 22 zasu gano adadin wadanda suka rasa rayukansu a lokacin hargitisn,su kuma gano hanyar da za'a hana irin haka sake afkuwa a Najeriya.Kazalika,hukumar zata kokarta binciko irin hasarar kadarorin da rikicin ya janyo.
Wata kungiyar kare hakkin Bil Adama ta Najeriya tayi kiyasin cewa akalla mutane dari biyar ne suka halaka a dalilin hargitsin siyasar.