Babban sakataren Majalisar Dinkin Duniya, MDD, Ban Ki-moon, ya yabawa Najeriya saboda zuba jarin da ta yi wajen kula da lafiyar mata da yara kanana.
A lokacin da ya fara rangadin kwanaki biyu a kasar da ta fi kowacce yawan jama’a a Afirka, Mr. Ban ya ziyarci wani asibiti jiya lahadi a Abuja, babban birnin kasar, ya kuma ce MDD zata tallafawa kokarin kyautata lafiyar al’ummar Najeriya.
Ya yabawa kasar a saboda kokarin da ta yi wajen hada hancin ayyukan lafiyar uwaye mata da na yara kanana da shirye-shiryen yaki da cutar SIDA, tarin fuka, maleriya da abinci mai gina jiki duk a wuri guda.
Har ila yau a jiya lahadi, Mr. Ban ya gana da shugaban hukumar zabe ta Najeriya, Attahiru Jega, ya kuma yabawa jami’an zabe a saboda shirya zabe mai inganci. Babban sakataren na MDD yace ‘yan kallo sun bayyana damuwa kan yadda aka gudanar da zaben shugaban kasa da na ‘yan majalisar dokoki da kuma na gwamnoni, amma kuma yana da kwarin guiwar cewa hukumar zaben zata binciko ta takali wadannan batutuwan.