WASHINGTON, D. C. - Kuma hakan na iya zama ƙarshen babi mafi sauki na shirin gwamnatin Biden na tsawon watanni biyu, na kashe dala miliyan 320 don buɗe hanyar teku don kai agajin jinkai zuwa Gaza, wanda ke dauke da haɗari da rashin tabbas ga tawagogin jigilar kayan agaji yayin da ake fama da karuwar tashin hankali da kuma rashin abinci tsakanin Falasdinawa.
Ga Shugaba Joe Biden, sabuwar gadar kan ruwa da mashigar da ma'aikatar tsaron Amurka ta Pentagon ke ginawa, wani kokari ne mai wahala, kuma wani yunƙuri na magance ƙalubalen da ake fuskanta wajen samar da kayan agaji a Gaza inda yaƙi ke dada tsanani baya kuma ga takunkumin da ƙawarta Isra'ila ta sanya a makatarar ƙasa tun bayan da Hamas ta kai munanan hare-hare kan Isra'il a watan Oktoba.
Maj. Janar Pat Ryder, sakataren yada labarai na Pentagon, ya fada jiya Talata cewa kungiyoyin agaji sun shirya don jigilar kayayyaki na farko ta hanyar tekun na Amurka.
"A cikin kwanaki masu zuwa, ku na iya sa ran ganin wannan habbosar na wakana. Kuma muna da yakinin cewa za mu iya, tare da hadin gwiwar kungiyoyin sa kai, ton tabbatar da cewa za a iya samar da kayan agaji,” inji shi.
-AP