Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Tawagar Hamas Za Ta kai Ziyara Birnin Alkahira


Gaza Afrilu 27, 2024,
Gaza Afrilu 27, 2024,

Tawagar Hamas za ta ziyarci birnin Alkahira a yau Litinin da nufin ganin an cimma matsayar tsagaita bude wuta, kamar yadda wani jami'in Hamas ya shaidawa kamfanin dillancin labarai na Reuters a ranar Lahadi.

WASHINGTON, D. C. - Hakan na faruwa ne yayin da masu shiga tsakani ke kara kaimi wajen cimma matsaya gabanin harin da Isra'ila ke sa ran kai wa a birnin Rafah da ke kudancin Gaza.

Jami'in wanda ya nemi a sakaya sunansa, ya ce tawagar za ta tattauna kan shawarar tsagaita bude wuta da Hamas ta mika wa masu shiga tsakani na Qatar da Masar, da kuma martanin Isra'ila.

Bai bayyana cikakkun shawarwarin na baya-bayan nan ba, amma wata majiya da aka yi bayani kan tattaunawar ta shaida wa kamfanin dillacin labarai na Reuters cewa ana sa ran Hamas za ta mayar da martani kan bukatun da Isra'ila ta gabatar a ranar Asabar.

Majiyar ta ce hakan ya hada da yarjejeniyar amincewa da sakin fursunonin da aka yi garkuwa da su fiye da 40 domin sakin Falasdinawa da Isra’ila ke tsare da su a gidajen yari da kuma mataki na biyu na sasantawa da ya hada da "lokacin dawwama cikin kwanciyar hankali" - martanin sulhu da Isra'ila ta yi kan bukatar Hamas domin tsagaita wuta na dindindin.

Majiyar ta ce bayan matakin farko, Isra'ila za ta ba da damar zirga-zirga tsakanin kudanci da arewacin Gaza da kuma janye wani bangare na sojojin Isra'ila daga Gaza.

Shugaban Amurka Joe Biden ya tattauna da Firaministan Isra'ila Benjamin Netanyahu a ranar Lahadin da ta gabata, kuma Fadar White House ta ce sun sake nazarin shawarwarin da aka tsara don ganin an sako mutanen da aka yi garkuwa da su tun bayan harin da Hamas ta kai kan Isra'ila a ranar 7 ga watan Oktoba tare da tsagaita bude wuta a Gaza.

Har ila yau, sun tattauna batun kara kai kayan agaji, ciki har da shirye-shiryen bude sabbin mashigar Gaza, a cewar shi.

-Reuters

Dandalin Mu Tattauna

Tambayoyin wasu ‘yan kasashen Afirka akan manufifi da Shugabancin Donald Trump ga kasashensu
please wait

No media source currently available

0:00 0:09:10 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
XS
SM
MD
LG