Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Kungiyar Agaji Ta World Central Kitchen, Ta Dakatar Da Ayyuka A Gaza Bayan Harin Isra'ila Da Ya Kashe Ma'aikata 7


ISRA’ILA/GAZA-World Central Kitchen
ISRA’ILA/GAZA-World Central Kitchen

Wani harin da Isra’ila ta kai ya kashe ma’aikatan jin kai bakwai da ke aiki da kungiyar abinci, lamarin da ya sa kungiyar ta World Central Kitchen ta dakatar da kai kayan agaji zuwa Gaza a ranar Talata, inda hare-haren Isra’ila ya jefa dubban daruruwan Falasdinawa cikin matsananciyar yunwa

WASHINGTON, D. C. - Kasar Cyprus, wacce ta taka muhimmiyar rawa wajen kokarin kafa hanyar teku domin kai abinci zuwa yankuna, ta ce jiragen ruwan da suka iso kwanan nan suna komawa baya dauke da kimanin tan 240 na kayan agajin da ba a kai ba.

Ba a iya tabbatar da tushen gobarar da yammacin ranar Litinin ba. Sojojin Isra'ila sun bayyana "bakin ciki na gaske" game da mutuwar yayin da suka gaza daukar alhakin lamarin.

Hotunan sun nuna gawarwakin, da dama sanye da kayan kariya masu dauke da tambarin kungiyar agaji ta World Central Kitchen, a wani asibiti a garin Deir al-Balah da ke tsakiyar Gaza.

World Central Kitchen (WCK), Gaza Afrilu 2, 2024. (Foto: REUTERS/Ahmed Zakot)
World Central Kitchen (WCK), Gaza Afrilu 2, 2024. (Foto: REUTERS/Ahmed Zakot)

Wadanda aka kashen sun hada da ‘yan kasar Birtaniya uku, da ‘dan Australiya, ‘dan kasar Poland, ‘dan Amurka da Kanada mai ‘yancin kasashen biyu da kuma Bafalasdine, kamar yadda bayanan asibiti suka nuna.

Kungiyar World Central Kitchen dai kungiyar agajin abinci ce ta shahararren mai dafa abinci José Andrés da ya kafa, ita ce mabuɗin hanyar da aka buɗe a cikin tekun kwanan nan, wanda ke ba da taimako ga arewacin Gaza, inda Majalisar Dinkin Duniya ta ce yawancin jama'a na gab da fuskantar yunwa, galibi sojojin Isra’ila sun yanke su daga shiga sauran yankin.

Andrés wanda kungiyar ta sa ke aiki a kasashe da dama da ke fama da yaƙe-yaƙe ko bala'o'i, ciki har da Isra'ila bayan harin 7 ga Oktoba wanda ya haifar da rikici na yanzu ya ce "ya yi matukar baƙin ciki" saboda mutuwar abokan aikinsa.

"Wajibi ne gwamnatin Isra'ila ta dakatar da wannan kisan gilla. Ya kamata a daina takaita agajin jin kai, a daina kashe fararen hula da ma’aikatan agaji, sannan a daina amfani da abinci a matsayin makami,” kamar yadda ya rubuta a kan shafinsa na X (Twitter).

WCK Gaza
WCK Gaza

Kungiyar agajin ta ce, tawagar na tafiya ne a cikin ayarin motoci guda uku da suka hada da wasu motoci sulke guda biyu, kuma an sanar da tafiyar motocin wa sojojin Isra'ila.

Rear Adm. Daniel Hagari, babban mai magana da yawun rundunar soji, ya ce jami'ai na "nazari akan lamarin a matakai mafi girma." Ya ce za a kaddamar da wani bincike mai zaman kansa wanda "zai taimaka mana wajen rage faruwar irin wannan lamari."

-AP

Dandalin Mu Tattauna

Tambayoyin wasu ‘yan kasashen Afirka akan manufifi da Shugabancin Donald Trump ga kasashensu
please wait

No media source currently available

0:00 0:09:10 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
XS
SM
MD
LG