Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Amurka Na Fatan Isira'ila Da Hamas Za Su Kwance Damara


Shugaba Joe Biden
Shugaba Joe Biden

Duk da cijewar da tattaunawar Isira'ila da Hamas ta yi, Amurka na fatan bangarorin biyu za su cimma jituwa kan sauran bambancin da ke tsakaninsu don a samu tsagaita wuta.

Fadar Shugaban Amurka ta White House jiya Talata ta bayyana fatan cewa, Isira’ila da Hamas za su iya cike duk wani gibi a tattaunawar tsagait wuta, kamar yadda Isira’ila ta yi gargadin cewa za ta iya zurfafa farmakinta a yankin kudancin Rafah na kudancin Gaza, idan tattaunawar ta kasa kaiwa ga sako mutanen da aka yi garkuwa da su.

Kakakin Majalisar tsaron kasa na Amurka John Kirby ya fada cewa “Bayanan tattaunawar matsayar bangarorin biyu na nuna cewa ya kamata su iya rufe sauran gibin da suka rage, kuma za mu yi duk abin da za mu iya don tallafa wa wannan tsari.”

Rundunar sojin Isira’ila ta fada jiya Talata cewa sojojinta sun kwace iko da yankin Gaza na mashigar Rafah da ke tsakanin Zirin Gaza da Masar, kwana guda da suka umarci dubun dubatar Falasdinawa da su fice daga yankin kuma tayi ta kai hare hare ta sama.

A halin da ake ciki kuma, hukumomin ayyukan jinkai na MDD sun ce an rufe mashigar mutane da kayayyaki na Rafah da Karem Shalom ta kowane bangare, wanda hakan ya katse kayayyakin bukata ga fararen hula sama da miliyan biyu a yankin Falasdinun da ke fama da rikici.

Jens Laerke, mai magana da yawun ofishin kula da ayyukan jinkai ya ce “A halin yanzu ba mu da wata kofa ta shiga Rafah kamar yadda COGAT ta hana mu damar shiga yankin don taimakawa."

COGAT it ace hukumar Isira’ila da ke daidaita ayyukan gwamnati a yankunan Falasdinawa.

Ya ce “Wannan yana nufin cewa an sake rufe mahimman wuraren shiga biyu don kai kayan agaji zuwa Gaza.”

Dandalin Mu Tattauna

XS
SM
MD
LG