Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Za Mu Bude Hanya A Teku Don Kai wa Falasdinawa Agaji - Biden


Shugaba Biden yayin da yake jawabin halin da kasa ke ciki a gaban gamayyar majalisun dokokin Amurka.
Shugaba Biden yayin da yake jawabin halin da kasa ke ciki a gaban gamayyar majalisun dokokin Amurka.

Biden ya kuma jaddada ‘yancin Isra’il na kare kanta daga mayakan Hamas yayin da ya yi kiran neman a tsagaita wuta a kuma saki mutanen da kungiyar ta Hamas take garkuwa da su.

Shugaban Amurka Joe Biden ya yi amfani da jawabinsa na halin da kasa ke ciki wajen bayyana shirinsa na kai wa Falasdinawa tallafi.

Biden ya kuma yi kira ga majalisar dokoki kan amincewa da tallafin da za a aikawa Ukraine sannan ya gargadi Amurkawa kan barazanar da tsohon Shugaba Donald Trump yake yi wa tsarin dimokradiyya.

“A wannan dare, muna masu alfaharin cewa hadin kanmu na nan daram! Yana kuma kara karfi.” Biden ya ce yayin jawabin na shekara-shekara.

Jawabin Biden na shekara-shekara
Jawabin Biden na shekara-shekara

Shugaba Biden ya kuma tabo batun shekarunsa da ake ta ka-ce-na-ce akai, inda ya caccaci Trump, wanda ake ganin da shi zai kara duba da cewa ga dukkan alamu shi jam’iyyar Republican za ta ba tikitin takara.

“Batun yawun shekaranmu ba shi ne a gabanmu ba, abin dubawa shi ne irin yanayin tunaninmu. kiyayya, fushi, ramuwar gayya duk tsoffin tunani ne. Amma ba za ka iya shugabantar Amurka ta irin wadannan tsoffin hanyoyi ba.”

Duk da cewa jawabin na Biden ba na yakin neman zabe ba ne, amma ya yi amfani da shi wajen aikawa da masu kada kuri’a sakon cewa: Trump babban barazana ne ga tsarin dimokrdiyya.

Shugaban na Amurka ya kuma tabo batun mamayar da magoya bayan Trump suka yi wa ginin majalisar dokokin Amurka a ranar 6 ga watan Janairu, a kokarin da suka yi na neman a sauya nasarar da ya samu a zaben 2020.

“Wanda na gada (Trump) da kuma wasunku a nan, sun yi kokarin yin rufa-rufa kan gaskiyar abin da ya faru a ranar 6 ga watan Janairu. Ni ba zan yi haka ba.”

Tsohon shugaban Amurka, Donld Trump
Tsohon shugaban Amurka, Donld Trump

Yayin da yakin da dakarun Isra’ila ke ci gaba da wakana a Gaza, Biden ya sanar da wani sabon tsari na kai tallafi ga Falasdinawa da ake matukar bukata.

“A wannan dare, in mai umartar dakarun Amurka, da su samar da wata mashiga a tekun meditareniya a gefen gabar tekun Gaza ta yadda za a iya shigar da kayayyakin abinci da ruwa da magunguna da kuma kayayyakin kafa matsuguni na wucin gadi. Amurka ba za ta tura dakarunta na kasa ba.”

Sai dai babu cikakkiyar masaniya kan ko wannan tsari zai farantawa ‘yan Democrat masu ra’ayin sauyi, da Larabawa da kuma Amurkawa Musulmi da suke fushi da yadda Biden yake nuna cikakken goyon baya ga Isra’ila. Daruruwan mutane ne suka yi zanga-zanga a wajen ginin majalisar dokokin yayin da Biden yake jawabin.

Biden ya kuma jaddada ‘yancin Isra’il na ta kare kanta daga mayakan Hamas yayin da ya yi kiran neman a tsagaita wuta a kuma saki mutanen da kungiyar ta Hamas take garkuwa da su.

Zauren Majalisar Dokokin Amurka
Zauren Majalisar Dokokin Amurka

A kuma wani lamari da ba a saba gani ba, Biden ya nunawa Isra’ila fushinsa kan rashin tura kayyakin agaji da kuma adadin mutum 30,000 da aka kashe a Gaza.

“Sakona ga shugbannin Isra’ila shi ne, bai kamata batun samar da kayayyakin agaji ga jama’a ya zama batu mara muhimmanci ba ko kuma wani abu da za a yi ciniki akansa. Yakamata batun kare rayukan mutanen da ba su ji ba ba su gani ba ya zama abu mai muhimmanci. Yayin da muke hangen gaba, maslaha ga wannan al’amari ita ce a samar da kasashe biyu.” Biden ya ce.

Tsare-tsaren sha’anin kasashen hulda da kasashen waje da Biden ya saka a gaba, na fuskantar kalubale daga ‘yan Republican da ke majalisar wakilai, wadanda suka dakile tallafin dala biliyan 95 ga Ukraine da majalisar dattawa ta amince da shi don taimaka mata a yakin da take yi da Rasha, inda ya yi kira da su amince da kudurin.

“Sakona ga Shugaba Putin wanda na sani da dadewa shi ne: Ba za mu juya baya mu tafi ba.”

Jawabin halin da kasa ke ciki
Jawabin halin da kasa ke ciki

Biden ya kuma yi kira ga ‘yan majalisar da su amince da wani kudurin doka kan batun shige da fice da kuma samar da tsaro akan iyaka – wani batu da ke da muhimmanci ga masu kada kuri’a.

Ya kuma dora laifin cikas din da ake samu wajen amincewa da kudurin akan ‘yan Republican da Trump inda ya zarge da su da siyasantar da batun.

“Bai kamata a ce muna fada akan batun iyaka ba. Ni a shirye nake na samar da mafita.” In ji Shugaba Biden.

Biden ya kuma sha alwashin samar da tsaro ga ‘yancin zubar da ciki da kuma hanyar haihuwa ta IVF – wani babban batu da ke damun ‘yan Democrat yayin da jihohin da ke karkashin mulkin ‘yn kwanzabative ke hana amfani da tsarin.

“Da yawa daga cikinku da ke wannan zauren majalisar da wanda na gada kuna alkawarin cewa za ku haramta ‘yancin walwalar hihuwa. Haba don Allah, wane ‘yancin walwala kuma kuke shirin hanawa.”

Biden ya kuma koda tsare-tsarensa, inda ya kwatanta tattalin arzikin Amurka a matsayin “abin kishi ga duniya”

Ya kuma zayyana ajandar samar da ci gaba ga tsarin tattalin arzikin Amurka, inda ya kaikaici manyan kamfanonin kasar.

“Bai kamata wani biloniya ya biya kudin harajin tarayyra kasa da abin da malamin makaranta ko mai aikin shara ko ma’aikacin jinya ke biya ba.”

Sanata Katie Britt ta jihar Alabama wcce ta yi jawabin mayar da martani ga jawabin Biden
Sanata Katie Britt ta jihar Alabama wcce ta yi jawabin mayar da martani ga jawabin Biden

Bisa al’adar jawabin na halin da kasa ke ciki, ‘yan bangaren adawa wato ‘yan Republican, na da hurumin su ma su yi jawabin mayar da martani, kuma a wannan shekara, Sanata Katie Britt ta jihar Alabama ce ta yi jawabin.

“Shugaba Biden sam bai fahimta ba. Ba ya tafiya da zamani. Iyalai sun shiga wahala karkashin mulkinsa. Babu tsaro a unguwanninmu, haka ma a kasarmu.”

Alkaluma dai sun nuna tattalin arzikin Amurka ya zarta yadda aka yi hasashe. Sai dai hauhawar farashin kakayyaki, ta zama wani batu da masu kada kuri’a ke kuka a kai – lamarin da ka iya zama matsala ga Biden yayin da aka tunkari zabe mai zuwa.

Dandalin Mu Tattauna

Tambayoyin wasu ‘yan kasashen Afirka akan manufifi da Shugabancin Donald Trump ga kasashensu
please wait

No media source currently available

0:00 0:09:10 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
XS
SM
MD
LG