WASHINGTON, D. C. - Yunwa dai na kara ta’azzara a yankin zirin Gaza kuma ba a kawo karshen yakin da aka shafe watanni biyar ana gwabzawa tsakanin Isra’ila da Hamas ba.
An gudanar da Sallah da addu'o'i a wajen baraguzan gine-gine da aka rusa da yammacin Lahadi. Wasu mutane sun rataye fitulun da kayan ado a cikin sansanonin tanti, aka kuma sa wani faifan bidiyo daga wata makarantar Majalisar Dinkin Duniya da aka mayar matsuguni ya nuna yara suna rawa da fesa kumfan wasa yayin da wani mutum ke rera waka a cikin lasifika.
Sai dai ba a yi wani gagarumin biki ba kamar yadda aka saba, sakamakon wannan yaki na watanni biyar da ya yi sanadin mutuwar Falasdinawa sama da 30,000 tare da barin yawancin Gaza cikin kango. Iyalai yawanci za su bude baki bayan azumin yau da kullun tare da liyafar biki, amma ko da akwai abinci, akwai kaɗan fiye da kayan abincin gwangwani kuma farashin ya yi yawa ga mutane da yawa.
"Ba ka ganin kowa da farin ciki a idanunsa," in ji Sabah al-Hendi, wanda ke siyayyar abinci ranar Lahadi a birnin Rafah da ke kudancin kasar. “Kowane iyali yana bakin ciki. Kowane iyali yana da shahidi wato wanda ya rasu a yakin.”
Kasashen Amurka, Qatar da Masar sun yi fatan kulla yarjejeniyar tsagaita wuta a daidai lokacin da ake gudanar da bukukuwan farin ciki kamar yadda aka saba yi na azumin daga safiya zuwa magariba, wanda zai hada da sakin dimbin mutanen Isra'ila da aka yi garkuwa da su, da kuma fursunonin Falasdinu, da shigar da kayan agaji, amma tattaunawar ta ci tura a makon jiya.
-AP
Dandalin Mu Tattauna