Shugaban Amurka na 47 din zai fara aiki nan take da jerin umarnin zartarwa da aka tsara domin matukar rage yawan bakin hauren dake shiga kasar.
Shugaba Joe Biden yayi afuwa ga Dr. Anthony Fauci da Janar Mark Milley mai ritaya da mambobin kwamitin Majalisar Wakilai da suka binciki harin da aka kaiwa Majalisar Dokokin Amurka na ranar 6 ga watan Janairu
Sa’ilin da zababben shugaban kasa Donald Trump ya karbi rantsuwar kama aiki a matsayin shugaban Amurka a babban dakin taro na Majalisar Dokokin Kasar ta Capitol, ya yi haka ne yana fuskantar mutum mutumin rabaran Martin Luther King a bisa tarihin hutun tunawa da King na tarayyar kasar, 20 Janairu
Zababben mataimakin shugaban kasa JD Vance ya karbi rantsuwar kama aiki kafin aka rantsar da Shugaban Trump.
Ana sa ran milyoyin Amurkawa zasu kalli yadda Trump, mai shekaru 78, zai sake karbar rantsuwar kama aiki a sabon wa’adin mulki na shekaru 4 a fadar White House yayin da Joe Biden, mai shekaru 82, zai bar fadar bayan kammala wa’adin mulki daya, ta akwatunan talabijin dinsu.
Hasashen fuskantar matsanancin sanyi a wunin yau Litinin ya sa Trump ya sa aka mai da bukin rantsarwar cikin majalisar dokokin Amurka sannan aka mai da faratin ban girman da aka saba yi a bukin rantsarwar Capital one Arena.
Trump ya ce yana Shirin fitar da wata dokar da zata baiwa kamfanin Tik Tok da shalkwatar ta take China damar neman wani wanda Amurka ta amince da shi za zai saye kamfanin Tik Tok kafin dokar haramcin ta fara aiki gadan gadan.
“Zamu Tabbata mun yi aikin da zai shafe koma bayan Da Amurka ta fuskanta na shekaru hudu (4) a ranar farko da muka kama aiki...
"Martin Luther King Jr. da Robert F. Kennedy Jr. sune mutanen da nake koyi da su a siyasa, Biden cikin jawabin shi na ban kwana a South Carolina sannan ya yiwa al'ummar jihar South Carolina godiya saboda irin goyon bayan da suka bashi.
Akalla mutane 600 ne ake sa ran za su halarci bikin da aka mayar Cikin Majalisar Dokokin Amurka saboda matsanancin sanyi sabanin yadda aka saba bukin a farfajiyar Majalisar dokokin Amurka.
Da yammacin ranar Asabar TikTok ya daina aiki a Amurka, kuma ya bace daga shagunan manhajojin Apple da Google, gabanin dokar da za ta fara aiki ranar Lahadi da ta bukaci a rufe manhajar da Amurkawa miliyan 170 ke amfani da ita.
Domin Kari
No media source currently available